"Haka Mu Ka Ji Labari:" 'Yan Kasuwa Sun Fadi Matsayarsu kan Karin Kudin Litar Fetur

"Haka Mu Ka Ji Labari:" 'Yan Kasuwa Sun Fadi Matsayarsu kan Karin Kudin Litar Fetur

  • Kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta bayyana cewa ita ma ta tsinci labarin karin farashin fetur ne kamar sauran yan kasa
  • Kungiyar ta amsa tambayar Legit kan ko ta kara farashin litar fetur bayan kamfanin NNPCL ya yi kari a dukkanin gidajen mansa
  • A martaninsa, Sakataren kudi na IPMAN, Musa Mai Kifi ya bayyana cewa NNPCL kamfani ne mai zaman kansa, su ma su na zaman kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta ce yadda yan kasar nan su ka ji labari, ita ma haka ta tsinci batun karin farashin litar fetur.

Kara karanta wannan

"A kashe mu a huta:" Yan Najeriya sun koka da karin farashin litar man fetur

Sakataren kudin IPMAN na kasa, Musa Yahaya Mai Kifi ne ya shaidawa Legit haka a tattaunarmu kan ko sun kara farashin litar fetur a kungiyance.

NNPCL
IPMAN ba ta kara farashin litar fetur ba Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

Jami'in na IPMAN ya kara da cewa su ma sun wayi gari ne da samun labarin cewa kamfanin NNPCL ya yanke hukuncin karin farashin litar fetur a gidajen mansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

IPMAN ta magantu kan karin kudin fetur

Sakataren kudi na kungiyar IPMAN na kasa, Musa Yahaya Mai Kifi ya tabbatar da cewa har yanzu ba su kara farashin litar fetur a kungiyance ba.

"Kuma NNPCL din nan kamfani ne da su ke zaman kansu kamar yadda mu ma mu ke zaman kanmu daban. Saboda haka su a na su lissafin ne su ka kara shi haka.
"Amma mu da yawa daga cikin mutanenmu ba wanda ya kara wannan farashin tukuna,"

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi dalilin kawo manufofin tattalin da suka jawo wahalar rayuwa

- Musa Yahaya Mai Kifi

Kungiyar IPMAN na tattaunawa da Dangote

A martaninsa kan ko za a samu saukin farashin litar fetur tun da kamfanin NNPCL ya ba yan kasuwa damar dauko fetur kai tsaye daga matatar Dangote, Musa Yahaya Mai Kifi ya ce ana tattaunawa a kai.

Ya tabbatar da cewa idan sun kammala tattaunawa kan farashin da matatar Dangote za ta sayar masu ne za su duba farashin da za su sayarwa yan kasar nan.

NNPCL: An samu karin farashin fetur

A baya mun wallafa cewa jama'ar kasar nan sun fuskanci karin farashin litar fetur a dukkanin gidajen mai mallakin NNPCL.

Ko a baya, kamfanin man na kasa ya yi gargadin cewa za a iya samun karuwar farashin litar fetur idan ya janye daga zama mai dakon fetur daga matatar Dangote kamar yadda wasu ke neman a yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.