Gwamnati Ta Caccaki Tsarin Buhari, An Fado Sharadin Samar da Jirgin Nigeria Air

Gwamnati Ta Caccaki Tsarin Buhari, An Fado Sharadin Samar da Jirgin Nigeria Air

  • Gwamnatin tarayya ta gano kurakurai da gwamnatin Muhammadu Buhari ta so yi wajen mallakawa kasar nan jirgin sama
  • Ministan harkokin sufurin jirgin sama, Festus Keyamo ya bayyana cewa da an ci gaba da yarjejeniyar, da kasar nan ta yi asara
  • Festus Keyamo ya bayyana yadda ya dace gwamnati ta samu jirgin sama na kanta wanda zai yi daidai da tsarin tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta caccaki tsarin da gwamnatin baya ta Muhammadu Buhari ta bi wajen kaddamar da jirgin sama mallakin kasar nan.

Ministan harkokin sufurin jirgin sama, Festus Keyamo ya bayyana matsayarsa kan yadda aka yi kokarin mallakawa Najeriya jirgin sama.

Kara karanta wannan

Dangote: Gwamnati ta fadi matata 1 da ta amince ta rika samar da man jiragen sama

Keyamo
Gwamnati ta caccaki tsarin samar da jirgin saman Najeriya Hoto: Festus Keyamo
Asali: Facebook

A hirarsa da Arise Television a ranar Talata, Festus Keyamo ya ce idan har za a kaddamar da jirgin sama mallakin kasar nan, yan Najeriya ya kamata su mallake shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda za a samar da jirgin sama na kasa

Jaridar The Cable ta wallafa cewa kamata ya yi a kaddamar da jirgin saman kasar nan yadda zai yi daidai da tattalin arziki.

Festus Keyamo bayyana cewa tsarin da gwamnatin baya ta dauko na samar da jirgin, zai jefa harkokin sufurin kasar nan hannun gwamnatin kasar waje.

"Da kuskure a samar da jirgin kasa:" Keyamo

Ministan harkokin sufurin jirgin sama na kasa, Festus Keyamo ya gano kura-kurai da gwamnatin Buhari ta kusa tafkawa wajen samar da jirgin sama mallakin Najeriya.

Ya bayyana cewa shirin gwamnatin tarayya a waccan lokaci da jirgin Ethiopian Airlines zai bukaci kasar nan ta rika biyan $112m duk shekara na hayar jirgin.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: Dattawan Arewa za su nemo hanyar magance matsalar tsaro

An kwace jiragen gwamnatin Najeriya

A wani labarin kun ji cewa kamfanin Zhongshang Fucheng ya kammala kwace wasu jiragen Najeriya biyo bayan samun sahalewar wata kotu da ke zamanta a kasar Canada.

Kamfanin Zhongshang Fucheng ya samu nasara a kotu kan Najeriya biyo bayan saba yarjejeniya, kotun ta sahale masa ya kwace jirage da wasu daga cikin kadarori mallakin kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.