‘Allah Ke ba da Mulki’: Malamin Musulunci Ya Dira kan Pantami kan Carbi, Ya ba Shi Shawara

‘Allah Ke ba da Mulki’: Malamin Musulunci Ya Dira kan Pantami kan Carbi, Ya ba Shi Shawara

  • Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan halacci ko haramcin jan carbi, Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya yi tsokaci game da lamarin
  • Sheikh Ishaq ya bayyana matsayarsa kan ingancin jan carbi ko akasin haka inda ya ce zai iya halatta kuma zai iya haramta
  • Hakan ya biyo bayan kalubalantar malamai da Farfesa Isa Pantami ya yi kan tattaunawa game hukuncin jan carbi a addini

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Malamin Musulunci ya yi tsokaci kan rigimar da ake game da halacci ko haramcin carbi a Musulunci.

Sheikh Ishaq Adam ishaq ya ce idan har zargin da Malam Idris Abdulaziz ya yi kan Farfesa Isa Pantami gaskiya ne to akwai matsala.

Kara karanta wannan

Gwamna ya rugurguza katafaren ginin babba a APC cikin dare, an fara cacar baki

Malamin Musulunci ya yi magana kan rigimar carbi a tsakanin Pantami da Idris Abdulaziz
Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya shawarci Farfesa Pantami kan rigimar carbi da Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi. Hoto: Karatuttukan Malaman Musulunci.
Asali: Facebook

Malami ya yi magana kan rigimar carbi

Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifian bidiyo da shafin karatuttukan malaman Musulunci ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Adam ya ce Malam Idris ya zargi Farfesa Pantami da sassautawa yan darika domin shirin takarar siyasa da ya ke yi a Gombe.

Barista Ishaq ya kara da cewa idan har zargin gaskiya ne to Pantami ya tafka kuskure saboda ya fi kowa sanin Allah ke ba da mulki ba sauka da hanya mai kyau ba.

Carbi: Sheikh Ishaq ya ba Pantami shawara

"Malam Isa Ali Pantami ya kalubanci masu ganin jan carbi bidi'a su zo su tattauna, Malam Idris Abdulaziz da Baffa Hotoro sun amsa gayyatarsa."
"Idris Abdulaziz ya burge ni, ya fadi dalilansa inda ya ce Pantami yana sassautawya yan darika saboda neman siyasa da yake yi."

Kara karanta wannan

'Mene dalilin kiran sunana kadai ', Gwamna ya kalubalanci Tinubu kan rigimar Ribas

"Idan har wannan ne dalili, babu abin da za mu yi wa Pantami sai tunatarwa saboda Allah na da ba da mulki ne ga wanda ya so."

- Sheikh Ishaq Adam Ishaq

Za a yi mukabala tsakanin Pantami da Dutsen Tanshi

Kun ji cewa magana ta kara dawowa sabuwa musamman a kafafen sadarwa kan matsayin amfani da carbi a addinin Musulunci.

Isa Ali Pantami ya ce amfani da carbi ba bidi'a ba ne kuma ya yi kira ga duk wanda yake ganin ba haka ba ne su zo a yi zaman kure.

A daya bangaren, Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya amsa gayyatar muƙabalar inda ya ambaci sharuda kan gudanar da ita.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.