"Ba dai N1,000 ba kuma": Farashin Litar Man Fetur Ya Sake Tashi a Najeriya
- Farashin man fetur ya sake yin tashin gwauron zabi a gidajen mai mallakin kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) da ke birnin tarayya Abuja
- Farashin kowace litar mai ya tashi daga N897 da ake sayarwa a gidajen man na kamfanin NNPCL da ke birnin tarayya Abuja a ranar Laraba
- Wannan ƙarin dai na zuwa ne bayan NNPCL ya kawo ƙarshen yarjejeniyarsa da matatar Dangote na zama mai shiga tsakani a cinikayyar fetur
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi a gidajen mai mallakin kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) da ke Abuja.
Farashin ya tashi zuwa N1,030 kan kowace lita a gidajen mai na kamfanin NNPCL da ke Abuja a ranar Laraba.
Wannan ci gaban na baya-bayan nan ya zo ne bayan da kamfanin NNPCL ya yanke shawarar kawo ƙarshen yarjejeniyarsa da matatar man Dangote.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farashin fetur a gidajen man NNPCL
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa gidajen man NNPCL da ke tsakiyar babban birnin tarayya Abuja, sun daidaita farashin man fetur zuwa N1,030.
Wata kwastoma da ta je siyan man mai suna Glory Okoye, ta tabbatar da cewa tuni aka canza farashin zuwa N1,030 kan kowace lita.
"Wannan abin dariya ne. Na lura cewa farashin kowace lita ya canza daga N897 zuwa N1,030."
- Glory Okoye
A wasu gidajen man da dama na NNPCL da ke unguwannin Wuse da Lugbe a birnin Abuja, farashin kowace lita ɗaya ya koma N1,030.
Karanta wasu labaran kan farashin fetur
- Farashin mai ka iya sauyawa da NNPCL ya fasa shiga tsakanin Dangote da dillalai
- Matatar Dangote: NNPCL ya dauki matakin da zai iya jawo sauyin farashin fetur
- Da alamu fetur zai sauka bayan karyewar farashi a kasuwar duniya, an gano dalili
Ba a tausayin talaka
Muhammad Auwal ya shaidawa Legit Hausa cewa ko kaɗan wannan ƙarin kuɗin man fetur ɗin bai dace ba a wannan halin da ake ciki.
"Ko kaɗan gwamnati ba ta tausayawa talakawa, kullum ƙara ɓullo da hanyoyin da za ta ƙuntata musu ta ke yi. Idan ba a yi wasa sai lita ta kai N1500."
- Muhammad Auwal
Dangote ya faɗi tallafin da gwamnati ta ba shi
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana tallafin da gwamnati ta ba shi wajen gina matata.
Aliko Dangote ya bayyana cewa an gina matatar man Dangote ne ba tare da samun wani tallafi daga gwamnati ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng