Yaki Zai Canza: An Dauko Salon Hana Yan Bindiga Yawo a Jihohin Arewa

Yaki Zai Canza: An Dauko Salon Hana Yan Bindiga Yawo a Jihohin Arewa

  • Ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana nasarorin da rundunar sojin Najeriya ke cigaba da samu kan yan bindiga
  • Bello Matawalle ya bayyana cewa suna shirye shiryen fito da wasu dabarun hana yan bindiga sakat a Arewa ta Yamma
  • Ministan ya ce zai kai ziyara wasu jihohin Arewa domin karfafa haɗaka da gwamnoni kan kokarin cin nasara kan yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi bayani kan salon yaki da masu garkuwa da mutane a Arewa ta yamma.

Bello Matawalle ya bayyana cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai sun samu cikakkiyar nasara kan yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Manyan yan siyasa a Arewa da aka zarge su da hannu a ayyukan ta'addanci

Bello Matawalle
Ministan tsaro zai ziyarci jihohi. Hoto: Bello Matawalle
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Bello Matawalle ya ce za su cigaba da karfafa sojojin Najeriya domin samun nasara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙoƙarin hana yan bindiga yawo a jihohi

Ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle ya ce za su tabbatar yan ta'adda sun daina yawo daga waje zuwa waje ko daga jiha zuwa jiha ba tare da hallaka su ba.

Bello Matawalle ya kara da cewa hana yan ta'adda motsi zai taimaka wajen kawar da su kuma za su tabbatar da hakan duk da suka da zargi da suke fuskanta.

Ministan tsaro ya nemi hadin kan al'umma

Peoples Gazette ta ruwaito cewa Bello Matawalle ya yi kira ga malaman addini, kungiyoyin fararen hula da sarakunan gargajiya kan yaki da yan bindiga.

Ya kuma yi kira ga gwamnoni da kan ba jami'an tsaro hadin kai wajen kawar da ta'addancin masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Matawalle: Bello Turji ya fadi mai daukar nauyin ayyukansu

Bello Matawalle zai ziyarci jihohi

A kokarin kawar da yan bindiga a Arewa, Bello Matawalle ya ce zai kai ziyara jihohin Katsina, Zamfara da Kebbi.

Bello Matawalle ya yi jawabin ne a jihar Sokoto inda ya mika godiya ga gwamna Ahmed Aliyu kan hadin kai da yake ba sojojin Najeriya.

An kama sarki da taimakon yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Katsina ta cafke wani basarake da ake zargi da taimakon yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Rahotanni sun nuna cewa yan sanda sun kama basaraken ne a yankin jihar Kaduna bayan samun bayanan sirri a kansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng