Asiri Ya Tonu: An Kama Sarkin da Yake Taimakon Yan Bindigar Arewa

Asiri Ya Tonu: An Kama Sarkin da Yake Taimakon Yan Bindigar Arewa

  • Rundunar yan sanda a jihar Katsina ta cafke wani basarake da ake zargi da taimakon yan bindiga masu garkuwa da mutane
  • Rahotanni sun nuna cewa yan sanda sun kama basaraken ne a yankin jihar Kaduna bayan samun bayanan sirri a kansa
  • Haka zalika basaraken ya fadi yan ta'adda da yake da alaka da su da kuma wasu miyagu da suke aikin taimakon yan bindiga tare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Rundunar yan sanda ta cafke wani basarake dan shekaru 45 kan zargin taimakon yan bindiga a Katsina.

An kama basaraken ne mai suna Usamatu Adamu a wani ƙauye a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun yi gaba da gaba da yan bindiga, an yi kazamin fada,an ceto mata

Yan sanda
An zargin basarake da taimakon yan bindiga. Hoto: Nigerian Police Force.
Asali: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa kakakin yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq ne ya bayyana lamarin ga manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama sarki da taimakon yan bindiga

Rundunar yan sanda a jihar Katsina ta kama basaraken Tambai Runka a karamar hukumar Safana.

Ana zargin cewa basaraken, Usamatu Adamu yana taimakawa yan bindiga masu garkuwa da mutane ne da bayanan sirri.

Sauran wandada suke taimakon yan bindiga

Bayan tsananta bincike, basaraken ya ambaci wasu mutane biyu, Rabe Sada da Nasiru Shua'ibu da suke aiki taimakon yan bindiga tare.

Mutane ukun sun bayyana a gaban yan sanda cewa suna taimakawa yan bindiga da bayanan sirri wajen garkuwa da mutane.

Babban dan bindiga da suke taimako

Basaraken da sauran mutanen sun bayyana cewa suna taimakawa wani jagoran yan bindiga, Umar da ya fitini al'umma da sace sace.

Kara karanta wannan

Asirin kishiya mai ganawa jarirai azaba ya tonu, yan sanda sun cafke ta

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa rundunar yan sanda ta ce har yanzu ana gudanar da bincike kan lamarin domin tabbatar da gaskiyar abin da yake faruwa.

An fatattaki yan bindiga a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan jihar Katsina ta samu gagarumar nasara kan yan bindiga masu garkuwa da mutane.

An ruwaito cewa lamarin ya faru ne yayin da wasu masu garkuwa dauke da makamai suka yi yunkurin sace wasu mutane da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng