Manyan Yan Siyasa a Arewa da Aka Zarge Su da Hannu a Ayyukan Ta’addanci
Najeriya tana cigaba da shan fama game da matsalar tsaro musamman a yankin Arewacin kasar wanda ya yi sanadin rasa rayuka da dukiyoyi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Arewa maso Gabas na cigaba da shan fama na matsalar Boko Haram yayin da yankin Arewa maso Yamma ke fama da matsalar yan fashin daji da masu garkuwa.
Yayin da tsaron ke kara ta'azzara, an zargi wasu manyan yan siyasa a Arewacin Najeriya da hannu a ta'addanci.
Legit Hausa ta lalubo muku wadanda aka zarga kan ayyukan ta'addanci:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Bello Matawalle
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya sha kare kansa game da zargin daukar nauyin ta'addanci a yankin Arewa.
Matawalle wanda shi ne karamin Ministan tsaro a Najeriya ya karyata gwamnatin jihar Zamfara kan zarginsa da take yi kan lamarin.
2. Dauda Lawal Dare
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara shi ma bai tsira ba game da zargin da wasu suke yi masa kan daukar nauyin ta'addanci bayan fitar da wasu takardu.
A wani rahoto an zargi Dauda Lawal game da hannu a ta'addanci wanda ya musanta ware makudan kudi saboda ba yan bindiga.
3. Sanata Shehu Buba
Sanata Shehu Buba da ke wakiltar Bauchi ta Kudu ya karyata zargin da gwamnatin jihar Bauchi ta yi masa kan daukar nauyin wani kasurgumin dan ta'adda zuwa aikin hajji.
Wannan bai rasa nasaba da takun-saka da sanatan ke yi da Gwamna Bala Mohammed tun bayan caccakar gwamnan da kuma tsige shi daga sarauta da aka yi a jihar.
Tasirin ayyukan ta'addanci a Arewa
Ayyukan ta'addanci musamman a Arewacin Najeriya ya yi matukar tasiri a cikin rayuwar yan yankin.
Lamarin ya daidaita kauyuka da dama tare da hana manoma zuwa gonakinsu wanda ya haddasa tsadar kayan abinci.
Yunkurin da gwamnati ke yi don magance matsalar tsaro
Gwamnatin Tarayya ta dauki matakai da dama domin kawo karshen ayyukan ta'addanci a yankin Arewa.
Daga ciki akwai karfafa jami'an tsaro da makamai da kuma umartan karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle da hafsoshin tsaro su koma yankin Arewa maso Yamma domin kawo karshensu.
Majalisar Musulunci ta kare sanata Shehu Buba
A baya mun baku labarin cewa Majalisar shari'ar addinin Musulunci a Najeriya ta ba Shehu Umar Buba kariya bayan an zarge shi da daukar nauyin ta'addanci.
Ana zargin Sanatan mai wakiltar jihar Bauchi ta Kudu da daukar nauyin wani kasungumin dan ta'adda zuwa aikin hajji a kasar Saudiyya.
Rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta fara binciken zargin, kuma an mika bayanai ga shugaban kasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng