Matawalle: Bello Turji Ya Fadi Mai Daukar Nauyin Ayyukansu

Matawalle: Bello Turji Ya Fadi Mai Daukar Nauyin Ayyukansu

  • Dan ta'addan nan da ya addabi mazauna Arewa maso Yamma, Bello Turji ta magantu kan zargin da ake yi wa Bello Matawalle na daukar nauyinsa
  • Wasu kungiyoyi da gwamnatin Dauda Lawal ta jihar Zamfara na zargin karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle na daukar nauyin ayyukan Turji
  • Amma a sabon bidiyon da ya saki, ya soki gwamnatin jihar Zamfara, tare da bayyana inda ya ke samun goyon bayan gudanar da ta'addancinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara - Kasungurmin dan ta'adda, Bello Turji ya yi magana kan zargi da ake yi wa tsohon gwamnan Zamfara, Bello Turji da daukar nauyin ayyukansu.

Kara karanta wannan

Yaki zai canza: An dauko salon hana yan bindiga yawo a jihohin Arewa

Bello Turji dai fitinannen dan ta'adda ne da ke jagorantar daruruwan miyagun matasa masu rike da mugayen magamai su na kai hare-hare yankunan Arewa maso Yamma.

matawale
Bello Turji ya wanke Bello Matawalle Hoto: @BelloMatawalle
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa a sabon bidiyon da ya saki, ya bayyana gaskiyar abin da ya sani kan wanda ke daukar nauyin miyagun ayyukan da su ke gudanarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bello Turji ya wanke Bello Matawalle

Dan ta'adda, Bello Turji ya wanke karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle daga zargin daukar nauyin ayyukan ta'addanci da su ke yi wa jama'a.

"Zargin da gwamna Dauda Lawal ke yi wa Bello Matawalle na daukar nauyin ta'addanci ba zai yi maganin komai ba."

Wa ke daukar nauyin Bello Turji?

Dan ta'addan nan da ya addabi mazauna Zamfara da kewaye, Bello Turji ya ce Allah SWT ne ke rike da su da ba su damar gudanar da ayyukansa kan jama'a.

Kara karanta wannan

Manyan yan siyasa a Arewa da aka zarge su da hannu a ayyukan ta'addanci

Ya bayyana haka ne a daidai lokacin da ake musayar yawu tsakanin gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara da Bello Matawalle, kowa na zargin dayan da daukar nauyin yan ta'adda.

Bello Turji ya magantu kan sojojin Najeriya

A baya mun wallafa cewa rikakken dan ta'addan nan, Bello Turjui ya bayyana cewa mutuwa ba ta tsorata shi, biyo bayan kokarin sojojin kasar nan na kawo karshensa da sauran yan ta'adda.

Sai dai duk da cika bakin da dan ta'addan ya yi, ya nemi zama da gwamnatin tarayya da ta jihar Zamfara a wani yunkuri na ganin an nemo hanyar dakatar da ayyukan ta'addanci a yankin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.