Majalisa Ta Tantance Shugaban Izala da Tinubu Ya ba Jagorancin Hukumar Hajji
- Majalisar dattawa ta amince da nada shugaban kungiyar Izala na jihar Kano ya riƙe shugabancin hukumar aikin Hajji ta kasa
- Shugaban kwamitin harkokin kasashen waje, Sanata Abubakar Sani Bello ya ce Farfesa Abdullahi Sale Usman zai cire kitse a wuta
- Farfesa Abdullahi Sale Usman Pakistan ya ce zai yi kokarin hada kan dukkan ma'aikatan NAHCON domin kawo cigaba a hukumar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta tantance Farfesa Abdullahi Sale Usman Pakistan a matsayin shugaban NAHCON.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Sheikh Pakistan a matsayin malamin addini na farko da zai jagoranci hukumar alhazai ta kasa.
Hukumar NAHCON ce ta wallafa yadda majalisa ta tabbatar da Sheikh Abdullahi Sale Pakistan a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa ta tantance shugaban Izala a NAHCON
Majalisar dattawa ta amince da shugaban Izala na Kano da Bola Tinubu ya saka jagorancin hukumar alhazai ta kasa.
Farfesa Abdullahi Sale Pakistan ya kasance shugaban hukumar alhazai ta jihar Kano daga 2019 zuwa 2023.
Sanatoci sun yabi shugaban hukumar Hajji
Shugaban kwamitin harkokin waje, Sanata Abubakar Sani Bello ya ce suna da tabbas kan cewa Sheikh Pakistan zai yi aiki tukuru.
Sanata Muhammad Adamu Aliero ya ce babu wanda ya cancanta ya zamo shugaban NAHCON a wannan lokacin kamar Sheikh Pakistan.
Haka zalika Sanata Shehu Buba Umar ya ce kwarewa da Sheikh Pakistan yake da ita za ta taimaka masa wajen jaogorantar hukumar.
Saleh Pakistan ya yi magana kan aikin NAHCON
Sheikh Abdullahi Sale Pakistan ya ce zai tabbatar da hadin kai a tsakanin dukkan ma'aikatan NAHCON a Najeriya.
Ya kuma kara da cewa hukumar NAHCON za ta yi aiki domin tabbatar da walwalar mahajjatan Najeriya.
Tinubu ya daidaita shugabannin majalisa da GCON
A wani rahoton, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya sauya lambar girmamawar da ya ba kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas.
Bola Tinubu ya canza hukuncin da ya yi a farko, ya ɗaga ƙimar Abbas zuwa lambar yabo ta GCON maimakon CFR da ya sanar a baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng