Tinubu Ya Fadi Dalilin Kawo Manufofin Tattalin da Suka Jawo Wahalar Rayuwa

Tinubu Ya Fadi Dalilin Kawo Manufofin Tattalin da Suka Jawo Wahalar Rayuwa

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi wa yan Najeriya bayanin dalilin da ya sa gwamnatinsa ta samar da wasu manufofinta
  • Yan kasar nan dai na kokawa da manufofin gwamnatin tarayya tun bayan da ta karbi mulki kimanin watanni 17 da su ka gabata
  • A bayaninsa, shugaban ya ce matakan da ya dauka sun taka muhimmiyar rawa wajen hana kasar nan fadawa mawuyacin hali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, AbujaShugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dalilin gwamnatinsa na daukar wasu matakan da su ka rikita tattalin arzikin kasar nan.

Shugaba Bola Tinubu wanda Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya wakilta ya bayyana haka ne a yayin taron akantoci na kasa, karo na 54 da ya gudana ranar Talata a Abuja.

Kara karanta wannan

"Duk kanwar ja ce:" Bola Tinubu ya gano yadda za a yaki rashawa a Najeriya

Bola Tinubu
Tinubu ya ce manufofinsa na farfado da tattalin arziki Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa shugaban kasar na ganin dole ce ta sa gwamnati daukar matakan sake fasalta tattalin arziki da yan kasar nan ke kuka a kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya fadi dalilin manufofinsa kan Najeriya

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya tattaro cewa Shugaban kasa Tinubu ya ce gwamnatinsa ta fitar da wasu manufofi ne domin kare tattalin arziki daga karasa tabarbarewa.

Ya kara da cewa kwalliya ta fara biyan kudin sabulu, domin an samu karuwar kudi kan kayan da ake sarrafawa a cikin gida na GDP a kwata na farko da na biyu na shekarar 2024.

Shugaban kasa Tinubu ya fadi amfanin manufofinsa

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa wasu daga cikin tsare-tsaren da ta dauka kan tattalin arziki sun fara rage hauhawar farashi da daidaita kasuwar canji a kasar nan.

Shugaba Bola Tinubu ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa alamu na nuna cewa za a samu karuwar masu zuba hannun jari a kasar saboda manufofin.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

Gwamnatin Tinubu na son kakkabe rashawa

A baya mun ruwaito cewa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana takaicin yadda cin hanci da rashawa ya yi katutu a Najeriya, wanda ya ke zargin ya hana kasar ci gaba.

Shugaban ya ce duk da aikin hukumomin yaki da rashawa ne su yaki mummunar halayyar, amma su ma yan kasa sai sun bayar da gudunmawa wajen tabbatar da raba Najeriya da cin hanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.