Dangote Ya Bayyana Tallafin da Ya Samu Wajen Gwamnati kan Gina Matatar Mai

Dangote Ya Bayyana Tallafin da Ya Samu Wajen Gwamnati kan Gina Matatar Mai

  • Alhaji Aliko Dangote ya yi magana kan tallafin da ya samu daga wajen gwamnati yayin da yake gina matatar man da ya mallaka
  • Shugaban rukunin kamfanonin na Dangote ya ce babu wani tallafi da ya samu daga gwamnati wajen gina matatar mai ƙarfin tace ganga 650,000 a rana
  • Dangote ya yi kira da a ƙara yawan ɗanyen man da ake samarwa a ƙasar nan domin ya wadaci sababbin matatun man da ake da su a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana tallafin da gwamnati ta ba shi wajen gina matatar mai.

Aliko Dangote ya bayyana cewa an gina matatar man Dangote ne ba tare da tallafin gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan PDP ya fadi hanyar da za a ceto Najeriya

Dangote ya gina matatar mai a Najeriya
Dangote ya ce bai samu tallafi ba daga gwamnati wajen gina matatar mai Hoto: Bloomberg
Asali: UGC

Dangote ya bayyana haka ne a yayin jawabinsa a wajen taron ƙungiyar masu matatun mai ta Najeriya (CORAN) a Legas, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Nation ta ce taron dai an yi masa taken, "Mayar da Najeriya matsayin mai fitar da albarkatun man fetur."

Dangote ya ba da shawarwari

Dangote, wanda ya samu wakilcin Mista Ahmed Mansur, ya ce akwai buƙatar karfafa gwiwar masu zuba jari domin cimma burin ƙasar nan na zama cibiyar tace albarkatun mai.

Ya jaddada muhimmancin tabbatar da samar da isashshen man da ake buƙata a koda yaushe tare da yin kira da a kawo ƙarshen jinginar da ɗanyen mai.

Dangote ya kuma yi kira da a ba da fifiko wajen samar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida da kuma ƙara yawan man da ake samarwa domin ya wadaci sababbin matatun man da ake da su.

Kara karanta wannan

Ana cikin tsadar rayuwa Tinubu ya fadi lokacin da 'yan Najeriya za su gode masa

Karanta wasu labaran kan matatar Dangote

Dangote ya samu shawara kan matatar mai

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon kakakin Goodluck Jonathan ya ba Aliko Dangote shawara kan matatar man da ya gina.

Ima Niboro ya buƙaci babban attajirin Afrikan da ka da ya mayar da hankali wajen samun riba daga matatar man da ke a jihar Legas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng