Jirage Sun Yi Taho Mu Gama, Ana Fargabar Rasa Rayukan Fasinjoji da Dama
- Ana fargabar rasa rayukan fasinjoji aƙalla 21 bayan jiragen ruwan da suke ciki sun yi taho mu gama a jihar Legas
- Hatsarin ya auku ne lokacin jiragen waɗanda kowanensu suka yi karo wanda hakan ya jawo suka kife a tsakiyar rafi
- Kakakin ƴan sanda ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce an samu nasarar ceto mutum 11 cikin waɗanda suka nutse
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Aƙalla fasinjoji 21 ne ake fargabar sun nutse a wani hatsarin kwale-kwale da ya auku a garin Imore da ke ƙaramar hukumar Amuwo-Odofin a jihar Legas.
Hatsarin jirgin na ranar Litinin ya auku ne lokacin da wasu kwale-kwale guda biyu kowannen su ɗauke da fasinjoji 16 suka yi karo da juna sannan suka kife a tsakiyar rafin.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda hatsarin jirgin ya auku
Benjamin Hundeyin ya bayyana cewa an kai rahoton lamarin ne ga ofishin ƴan sanda na Ilashe da misalin ƙarfe 7:00 na daren ranar Litinin, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
A cewarsa, jami’an bayar da agajin gaggawa sun garzaya wurin da lamarin ya auku tare da ceto fasinjoji 11 waɗanda suka samu raunuka.
Ya ƙara da cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin sojin ruwa da ke garin Alakija domin kula da lafiyarsu.
Kakakin rundunar ƴan sandan ya bayyana cewa ana ƙoƙarin ceto sauran fasinjojin da ke cikin jiragen ruwan waɗanda ba a san inda suke ba har yanzu.
Wani jirgin ruwa ya kife da fasinjoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya gamu da hatsari a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Gabas na Najeriya.
Aƙalla mutane 41 da suka haɗa da mata da yara suka rasu bayan jirgin ruwan mai ɗauke da fasinjoji 53 ya kife a garin Gummi ta jihar Zamfara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng