Baya Ta Haihu: Hukumar Alhazai Za Ta Mayar da Kudi ga Mahajjatan 2024
- Gwamnatin tarayya za ta mayar da wani kaso daga cikin kudin hajjin bana ga alhazan kasar nan bayan an gano matsaloli
- Hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ce ta bayyana haka, inda ta ce ba a kyautatawa alhazan bana yadda ya dace ba
- Jami'ar hulda da jama'a ta NAHCON, Fatima Usara ta bayyana cewa alhazai N95,000 za su samu wani kaso na kudin hajjinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta gano yadda aka yi algus wajen kula da mahajjatan 2024, inda yanzu haka ake shirin biyan wani kaso na kudin aikin hajji ga alhazan.
Jami'ar hulda da jami'ar hukumar NAHCON, Fatima Usara ce ta bayyana haka a sanarwar da ta fitar jim kadan bayan taron da ya gudana a Abuja ranar Litinin.
Jaridar The Cable ta wallafa cewa an gudanar da taron da masu ruwa da tsaki a na aikin hajji, ciki har da ma'aikatan hukumar da na kamfanoni masu zaman kansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NAHCON za ta mayar da kudi ga alhazai
Jami'ar hulda da jama'a ta hukumar NAHCON, Fatima Usara ta bayyana cewa za a mayarwa alhazai 95,000 wani kaso da kudin da su ka biya na aikin hajjin 2024.
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa wannan ya biyo bayan gano cewa alhazan ba su samu kulawar da ta dace a lokacin gudanar da aikin hajjin wannan shekarar ba.
Nawa NAHCON za ta ba alhazai?
Hukumar alhazai ta kasa ta ce za a biya kowane daga cikin alhazai 95,000 da su ka gudanar da aikin hajjin bana Riyal 150, wanda ya yi daida da N67,000.
Hukumar ta cimma matsayar bayan taron da mukaddashin shugaban hukumar, Abdullahi Saleh ya jagoranta a ranar Litinin.
NAHCON: Gwamnati ta janye tallafin hajji
A baya mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta dakatar da biyan tallafi ga alhazan kasar nan da ke da niyyar ziyartar Saudiyya domin sauke farashi, domin a cewarta ba za ta iya ba.
Jami'ar hulda da jama'a ta hukumar NAHCON, Fatima Usara ce ta sanar da matakin gwamnatin, wanda hakan a nufin akwai fargabar mahajjatan bana za su biya kudin aikin hajji da tsada.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng