Yan Bindiga Sun yi Kwanton Ɓauna ga Askarawan Zamfara, Sun Kashe da Dama

Yan Bindiga Sun yi Kwanton Ɓauna ga Askarawan Zamfara, Sun Kashe da Dama

  • Askarawan da gwamnatin jihar Zamfara ta dauka domin taimakawa jami'an tsaro sun hadu da mummunan tsautsayi
  • An ruwaito cewa wasu yan bindiga ne suka yi kwanton ɓauna suka kai hari kan askarawan wanda ya jawo mutawar rayuka
  • Rahotanni sun nuna cewa mugun lamarin ya faru ne a wani yanki na karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Askarawan da gwamnatin Zamfara ta samar domin yaki da yan bindiga sun hadu da tsautsayi.

An ruwaito cewa yan bindiga sun yi kwanton ɓauna ga askarawan yayin da suke kokarin fita aiki da safe.

Dauda Lawal
An kashe askarawa a Zamfara. Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Rahoton Channels Television ya nuna cewa shugaban askarawan na jihar Zamfara ne ya bayyana yadda yan bindigar suka kai harin.

Kara karanta wannan

Asirin kishiya mai ganawa jarirai azaba ya tonu, yan sanda sun cafke ta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kashe askarawa 8 a Zamfara

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da cewa yan bindiga sun kashe askarawa takwas da aka kai aiki karamar hukumar Tsafe.

Shugaban askarawan jihar, Birgadiya Janar Muhammad Lawal (Mai ritaya) ne ya fitar da sanarwa ga manema labarai.

Yadda aka kashe askarawan Zamfara

Shugaban askarawan ya bayyana cewa suna fita aiki a karamar hukumar Tsafe ne da safe sai su tashi da misalin karfe 6:30 na yamma.

Yayin da suka fito aiki da safe, sun ajiye jami'ansu mota ta tafi dauko sauran sai yan bindigar da suka buya a cikin jeji suka fara harbinsu har suka kashe mutane takwas.

Dalilin kai askarawa yankinTsafe

Shugaban askarawan ya bayyana cewa an kai su tsafe ne domin bayar da tsaro a kan hanyar Gusau zuwa Funtua bayan an yawaita sace mutane.

Kara karanta wannan

Fargabar barkewar ambaliya: Gwamnati ta aika sakon gaggawa ga mazauna jihar Kwara

Tun bayan ajiye askarawa a kan hanyar watanni biyu da suka gabata yan bindigar suka daina satar mutane a wajen

An fatattaki yan bindiga a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan jihar Katsina ta samu gagarumar nasara kan yan bindiga masu garkuwa da bayin Allah.

An ruwaito cewa lamarin ya faru ne yayin da wasu masu garkuwa dauke da makamai suka yi yunkurin sace wasu mutane da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng