Yan Sanda Sun Yi Gaba da Gaba da Yan Bindiga, An Yi Kazamin Fada, An Ceto Mata

Yan Sanda Sun Yi Gaba da Gaba da Yan Bindiga, An Yi Kazamin Fada, An Ceto Mata

  • Rundunar yan sandan jihar Katsina ta samu gagarumar nasara kan yan bindiga masu garkuwa da mutane a ƙananan hukumomi
  • An ruwaito cewa lamarin ya faru ne yayin da wasu masu garkuwa dauke da makamai suka yi yunkurin sace wasu mutane da dama
  • Kakakin yan sanda a jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq ya yi karin haske kan yadda suka samu nasara kan miyagu yan bindigar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Rundunar yan sanda ta samu nasara kan yan bindiga masu garkuwa da mutane a ƙananan hukumomi biyu.

An ruwaito cewa yan sanda sun kai farmaki kan yan bindigar ne yayin da suka samu kiran gaggawa.

Kara karanta wannan

Yan daba sun cinna wuta a ƙananan hukumomin Rivers, sun yi fashe fashe

Yan sanda
Yan sanda sun ceto mutane a Katsina. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa yan sanda sun yi nasarar ceto mutane da aka yi yunkurin sacewa a kananan hukumomin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi fada da 'yan bindiga Dan Musa

Yan sanda sun bayyana cewa da misalin karfe 11:00 na rana yan sanda suka samu kiran gaggawa daga ƙauyen Matarau a karamar hukumar Dan Musa.

Yan bindigar sun zo da makamai ne domin yunkurin sace wasu mata amma yan sanda suka tunkare su suka gwabza gaba da gaba.

Jami'an Yan sanda sun samu nasara a Faskari

Haka zalika a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba yan sanda suka samu kiran gaggawa daga karamar hukumar Faskari.

Da misalin karfe 2:30 na rana yan bindiga suka tare hanya a ƙauyen Unguwar Kafa da niyyar sace wasu mata da yara kanana amma yan sanda suka wargaza su.

Kara karanta wannan

An cafke matashin da ya sassara dan banga har lahira, ya yi masa sata

Yan sanda sun ceto mutane a Katsina

Tribune ta wallafa cewa yan sanda sun yi musayar wuta da yan bindigar kafin yan ta'addar su ruga da gudu bayan sun ji wuta.

Hakan ya jawo yan sanda suka ceto mutane takwas daga sharrin yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Kakakin yan sanda, ASP Abubakar ya bayyana cewa yan bindigar sun gudu bayan sun samu munanan raunuka a sanadiyyar wutar da yan sanda suka bude musu.

'Yan sanda kama mata mai zaluntar jarirai

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Adamawa ta zargi wata kishiya da laifin azabtar da jarirai bisa zalunci.

An ruwaito cewa matar da ake zargin mai suna Fatima Abubakar tana zaune ne a ƙaramar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng