Farashin Mai Ka Iya Sauyawa da NNPCL Ya Fasa Shiga Tsakanin Dangote da Dillalai

Farashin Mai Ka Iya Sauyawa da NNPCL Ya Fasa Shiga Tsakanin Dangote da Dillalai

  • Kamfanin mai na NNPCL ya tsame kansa daga shiga tsakani a harkar kasuwancin man fetur a matatar Aliko Dangote
  • Kamfanin ya dauki matakin domin gudun biyan raran kudi yayin da ya ke shiga tsakanin dillalan mai da matatar Dangote
  • Wasu masana sun yi hasashen ba dillalan mai damar alaka kai tsaye da matatar Dangote ka iya kara farashin fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Masana sun yi hasashen za a yi iya samun tashin farashin mai a Najeriya.

Hakan bai rasa nasaba da matakin da kamfanin NNPCL ya dauka tsakaninsa da matatar Dangote.

Ana hasashen samun karin farashin mai bayan matakin NNPCL
Kamfanin NNPCL ya janye daga shiga tsakanin matatar Aliko Dangote da dillalan mai. Hoto: NNPC Limited, Dangote Industries.
Asali: Facebook

NNPCL ya fasa shiga tsakanin Dangote da dillalan mai

Kara karanta wannan

Matatar Dangote: NNPCL ya dauki matakin da zai iya jawo sauyin farashin fetur

Daily Trust a cikin wani rahoto ta ce kamfanin ya dauki matakin janye jikinsa game da shiga tsakani kan cinikayyar mai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan zai ba dillalan mai damar ciniki babu shamaki tsakaninsu da matatar man Dangote a Najeriya.

Matakin da NNPCL ya dauka zai dakile raran kudi da ya ke biya tsakanin farashin Dangote zuwa na yan kasuwa.

A yanzu, dillalan mai za su iya ciniki kai tsaye da matatar Aliko Dangote domin siyan mai daga gare ta, cewar rahoton Punch.

"Ba za mu cigaba da daukar nauyin biyan raran kudin ba a yanzu a harkokin mai na matatar Dangote da dillalai."

-Wani jami'in kamfanin NNPCL

Halin da aka shiga bayan kara kudin mai

Hakan ya biyo bayan karin farashin man fetur da kamfanin NNPCL ya yi wanda ya jefa al'umma cikin matsanancin hali.

Kara karanta wannan

Da alamu fetur zai sauka bayan karyewar farashi a kasuwar duniya, an gano dalili

A watan Satumbar 2024, NNPCL ya kara kudin daga N568 zuwa N855 inda wasu gidajen mai ke siyarwa fiye da N1,000 kan lita ɗaya.

An yi hasashen faduwar farashin mai

A wani labarin kuma, a baya an ce farashin mai na iya faduwa bayan farfadowar darajar Naira a karshen watan Satumbar 2024.

Manyan dillalan mai a Najeriya ne suka yi wannan hasashe inda suka ce farashin danyen mai ya fadi a kasuwar duniya.

Wannan na zuwa ne yayin da ake cikin mummunan yanayi na tsadar rayuwa tun bayan karin farashin mai da kamfanin NNPCL ya yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.