Gwamna Ya Amince da Karin Albashi, Ma'aikata Za Su Samu Fiye da N70,000
- Gwamnatin jihar Kogi ta bayyana shirinta na farantawa ma'aikatan jihar ta hanyar fara biyansu mafi karancin albashi
- Gwamna Ahmed Ododo ya bayyana haka a lokacin da ya ke yi wa ma'aikatan jiharsa albishir game da karin albashinsu
- Ya kuma bayyana lokacin da za a fara biyansu mafi karancin albashin N72,500 bayan karbar rahoton kwamitin albashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kogi - Gwamnatin jihar Kogi ta na shirin faranta wa ma'aikatanta, musamman a cikin halin tsada da hauhawar farashi.
Gwamna Ahmed Ododo ya amince da fara biyan mafi karancin albashin N72, 500 ga dukkanin ma'aikatan gwamnati.
Jaridar Nigerian Tribune ta tattara cewa gwamnatin Kogi ta kuma bayyana wa ma'aikata lokacin da za su fara karbar sabon mafi karancin albashin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma gwamnan ya bayyana dakatar da karbar haraji daga wurin ma'aikatan na tsawon shekara daya.
Za a fara biyan mafi karancin albashi a Kogi
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa gwamnan Kogi, Ahmed Ododo ya yi wa ma'aikata albishir da fara karbar mafi karancin albashi na N72,500.
Gwamnan ya fadi haka ne lokacin da ya karbi rahoton kwamitin mafi karancin albashi a jihar, karkashin jagorancin Elijah Evinemi.
Yaushe za a fara biyan sabon mafi karancin albashi?
Gwamna Ahmed Ododo ya yi albishir da fara biyan albashin ma'aikatan gwamnatin jihar nan take, watau a watan Oktoba domin inganta rayuwarsu.
Gwamnan ya tabbatar da cewa biyan mafi karancin albashin N72,500 ba alfarma ba ce, amma hakki na ma'aikata da gwamnati ta ba su.
Za a fara mafi karancin albashi a Oyo
A baya kun ji cewa gwamnatin jihar Oyo karkashin jagorancin Seyi Makinde ta yi alkawarin fifita jin dadin ma'aikatan jihar ta fara yunkurin biyansu mafi karancin albashi.
Gwamna Makinde ya ce da zarar batun karin da za a yi ya daidaita, ma'aikatan jihar za su fara karbar N72,000 a matsayin mafi karancin albashi kamar yadda aka tsara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng