Badakalar NYSC: Daga Karshe Ministar Tinubu Ta Fadi Laifin da Ta Yi
- Hannatu Musa Musawa ta fito ta yi magana kan ce-ce-ku0cen da ake yi dangane da batun ba ta yi wa ƙasa hidima (NYSC) ba
- Ministar al'adu da tattalin arziƙin fikirar ta bayyana cewa ko kaɗan babu wata doka da ta karya kafin a ba ta muƙamin minista
- Musawa ta bayyana cewa kotu ta riga da ta yi hukunci kuma nan gaba za ta bayyana yadda komai ya faru ga ƴan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministar al’adu da tattalin arziƙin fiƙira, Hannatu Musa Musawa, ta yi magana dangane da ce-ce-ku-cen da ake yi kan batun cewa ba ta yi NYSC ba.
Hannatu Musa Musawa ta bayyana cewa ba ta karya wata doka a muƙamin ministan da shugaba Bola Tinubu ya ba ta ba.
NYSC: Ministar Tinubu ta kare kanta
Ministar ta bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar talabijin ta Channels a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Vanguard da ta bibiyi tattaunawar ta ce lokacin da aka yi mata tambaya kan batun NYSC, sai ta kada baki ta ce babu wata doka da ta karya.
Ku tuna cewa ministar ta fuskanci suka kan rashin kawo shaidar kammala NYSC a lokacin da ake tantance ta a majalisar dattawa.
Me Hannatu ta ce kan batun NYSC?
Da take magana a kan lamarin, Hannatu Musawa ta ce niyyarta ita ce ta mayar da hankali kan ayyukan da gabanta a ofis maimakon yin magana kan dambarwar.
"Kotu ta riga da ta yanke hukunci. Wata rana zan fito na faɗi yadda komai yake. Wataƙila na yi NYSC fiye da kai (mai gabatarwa). Na yi NYSC aƙalla biyu a rayuwata."
"Ina ganin bashin da ƴan Najeriya ke bi na shi ne na fito na ce ban yi wani laifi ba. Ban karya doka ba. Na yi NYSC, na gama. Abin da zan iya gaya muku ke nan. Duk abin da na yi bisa doka ne."
- Hannatu Musa Musawa
Hannatu ta magantu kan canza ministoci
A wani labarin kuma, kun ji cewa Hannatu Musawa, ta yi magana kan shirin garambawul da shugaba Bola Tinubu yake yi wa majalisar ministocinsa.
Hannatu Musa Musawa ta ce ba ta damu da shirin yin sauyin da shugaban ƙasan yake son yi a majalisar ministocin ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng