Yunwa: Buhunan Shinkafar Tinubu Sun Isa Katsina, An Fara Rabawa Talakawa

Yunwa: Buhunan Shinkafar Tinubu Sun Isa Katsina, An Fara Rabawa Talakawa

  • Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fara raba tallafin shinkafa ga mazauna jihar Katsina domin ragewa jama'a radadin yunwa
  • Umaru Dikko Radda ne ya jagoranci kaddamar da rabon buhunhunan shinkafar tare da Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu
  • Sun bayyana cewa rabon shinkafar na daga cikin manufar gwamnatin tarayya na rage radadin yunwa da talakawan kasa ke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina - Gwamnatin tarayya ta kai buhunan shinkafa Katsina domin rabawa ga talakawan jihar da nufin rage radadin rayuwa.

Gwamna Umaru Dikko Radda na jihar ne ya kaddamar da rabon tallafin shinkafar ta cikin shirin gwamnatin Bola Tinubu na rage yunwa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi illar gobarar kasuwa ga Kano, Abba ya yi wa 'yan kasuwa alkawari

Dikko Radda
An fara raba shinkafar Tinubu a Katsina Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

A sakon da Sakataren yada labaran gwamna Radda, Ibrahim Kaula Mohammed ya wallafa a shafinsa na Facebook, an ji za a raba shinkafa buhuna 21, 924 ga mazauna Katsina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibrahim Kaula Mohammed ya bayyana cewa gwamnatin Katsina ta bullo da dabarun taimakawa manoma domin rage yunwa a fadin jihar.

Za a raba shinkafar Tinubu a Katsina

Channels Television ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta ce za a raba buhunhunan shinkafa ga mata da marayu da ke jihar Katsina.

Gwamnan Katsina, Umaru Dikko Radda da ya bayyana haka ya kara da cewa shinkafar za ta kai ga marasa karfi a mazabu 6,652 na jihar.

Minista ya fadi manufar raba shinkafa a Katsina

Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Abubakar Bagudu ya bayyana cewa rabon tallafin shinkafa na cikin hanyar rage yunwa a kasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara rabawa matasa Keke Napep 2000 marasa amfani da fetur

Ministan ya yaba da kokarin gwamnatin jihar Katsina wajen jajircewa da taimakon masu karamin karfi a halin yunwa da ake ciki.

Gwamnatin Tinubu za ta saida shinkafa a N40, 000

A wani labarin kuma gwamnatin tarayya ce ta bayyana shirinta na sayar wa da ma'aikatanta buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 a kan N40, 000.

Amma babu ma'aikacin da gwamnati za ta sayar wa da shinkafa har sai ya cika wasu sharudda, daga ciki har da mallakar katin shaidar dan kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.