Bayan Fubara, Wani Gwamnan Ya Rantsar da Ciyamomin APC, Ya Ba Su Shawarwari

Bayan Fubara, Wani Gwamnan Ya Rantsar da Ciyamomin APC, Ya Ba Su Shawarwari

  • Mai girma Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya rantsar da sababbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi 23 na jihar
  • Gwamna Hyacinth Alia ya rantsar da shugabannin ƙananan hukumomin ne bayan sun samu nasara a zaɓen da aka yi a ranar Asabar
  • Alia ya yi kira a gare su da su haɗa kai da gwamnatin jihar domin samar da romon dimokuraɗiyya ga mutanen yankunansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya rantsar da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi 23 na jihar.

Gwamna Alia ya rantsar da shugabannin ƙananan hukumomin ne a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoban 2024.

Gwamna Alia ya rantsar da ciyamoni a Benue
Gwamna Alia ya rantsar da ciyamomi 23 a Benue Hoto: Fr. Hyacinth Iormem Alia
Asali: Facebook

Jaridar Tribune ta rahoto cewa gwamnan ya rantsar da sababbin shugabannin ne a sabon ɗakin taro na gidan gwamnatin jihar da ke birnin Makurdi.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan PDP ya fadi hanyar da za a ceto Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara gwamnan ya ba su?

Gwamna Alia ya buƙace su da su yi aiki tare da ƴan adawa ta hanyar karɓar shawarwari da gyare-gyare masu ma'ana domin samar da shugabanci nagari.

Ya kuma buƙace su gudanar da mulki bisa gaskiya ba tare da nuna tsoro ko ƙoƙarin fifita wasu ba, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da wannan.

Gwamnan ya kuma yi kira gare su da su haɗa kai da gwamnatin jihar domin gudanar da ayyukan da mutanen yankunansu za su amfana da su.

"Gare ku sababbin zaɓaɓɓun ciyamomi, nauyin da ke kanku yana buƙatar ku yi aiki tuƙuru, samar da shugabanci mai kyau ba tare da nuna tsoro ko fifita wasu ba."
"Wannan nauyin da ke kanku yana buƙatar gaskiya, hangen nesa da jajircewa a dukkanin abubuwan da za ku yi."
"Ina shawartar ku da ka da mu maida hankalin kan abin da za ku samu, maimakon hakan ku fifita samarwa mutanenku romon dimokuraɗiyya."

Kara karanta wannan

Ana cikin tsadar rayuwa Tinubu ya fadi lokacin da 'yan Najeriya za su gode masa

- Gwamna Hyacinth Alia

Jam'iyyar APC ta lashe zaɓe a Benue

A wani labarin kuma, kun ji jam’iyyar APC mai mulki ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi da kansiloli a zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi a jihar Benue.

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi 23 da na kansiloli 276 a zaɓen da aka gudanar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng