Rikici Ya Barke a Ribas, 'Yan Bindiga Sun Farmaki Sabon Shugaban Karamar Hukuma

Rikici Ya Barke a Ribas, 'Yan Bindiga Sun Farmaki Sabon Shugaban Karamar Hukuma

  • An samu tashe tashen hankula a wasu kananan hukumomin jihar Ribas jim kadan bayan da rundunar 'yan sanda ta janye jami'anta
  • An rahoto cewa 'yan bindiga sun bude wuta kan mai uwa da wabi a sakatariyar karamar hukumar Ikwere a ranar Litinin dinnan
  • An ce 'yan bindigar sun fatattakin sabon shugaban karamar hukumar, Isreal Abosi daga sakatariyar yayin da ya yi shirin kama aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ribas - Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun bude wuta kan mai uwa da wabi a sakatariyar karamar hukumar Ikwere da ke jihar Ribas.

An ce an samu tashe tashen hankula a sakatariyoyin kananan hukumomin Ribas bayan rantsar da sababbin ciyamomi da kansiloli ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Ribas: Mummunar gobara ta babbake sakatariyar karamar hukuma, bayanai sun fito

'Yan bindiga sun kai farmaki karamar hukumar Ikwere da ke jihar Ribas
Ribas: 'Yan bindiga sun fatattaki ciyaman a lokacin da suka farmaki sakatariyar karamar hukuma. Hoto: @SimFubaraKSC
Asali: Twitter

An farmaki ciyaman a jihar Ribas

Wakilin jaridar The Guardian ya rahoto cewa 'yan bindiga sun fatattaki zababben shugaban karamar hukumar Ikwere, Isreal Abosi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan farmakin da 'yan bindigar suka kai, an ce masu zanga zanga sun kuma mamaye titunan jihar Ribas suna nuna adawa da rantsar da ciyamomin.

Anji masu zanga zangar na cewa, "Babu Wike babu jihar Ribas, babu Wike babu sakatariya" wanda hakan ya kara tabbatar da zargin da ake yi.

Rikici ya barke a garuruwan Ribas

Hakazalika, jaridar The Punch ta rahoto cewa an samu tashe tashen hankula a kananan hukumomi da dama ciki har da Oyigbo, Khana da Obio-Akpor.

Ana ganin cewa wadannan rigingimun ba sa rasa nasaba da janye jami'an 'yan sanda da aka yi daga tsaron dukkanin sakatariyoyin kananan hukumomin jihar.

Kara karanta wannan

Ribas: Gwamna zai rantsar da 'yan jam'iyyar adawa da suka lashe zaben ciyamomi

An ga ma’aikatan kananan hukumomin da suka nuna jin dadinsu kan sake bude sakatariyoyin tare da komawa bakin aiki suna tururuwar gudun tsira da rayukansu.

A halin da ake ciki, wata rundunar tsaro ta shawarci mazauna jihar da su guji sakatariyoyin kananan hukumomin jihar a cikin kwanaki masu zuwa saboda dalilan tsaro.

Ribas: An cinnawa sakatariya wuta

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu bata gari sun cinnawa sakatariyar karamar hukumar Eleme da ke Ribas awanni bayan rantsar da sababbin ciyamomi.

Sabon zababben ciyaman na Eleme, Hon. Brain Gokpa ya isa sakatariyar tare da kansiloli da magoya bayansa inda ya tarar da an kona gine-ginenta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.