An yi Gumurzu da Yan Bindigar da Suka so Sace Matar Dan Majalisa, An Kashe Miyagu

An yi Gumurzu da Yan Bindigar da Suka so Sace Matar Dan Majalisa, An Kashe Miyagu

  • Yan sandan Najeriya sun tafka kazamin fada da yan bindigar da suka yi yunkurin sace matar dan majalisa a yankin Warri na jihar Delta
  • Rundunar yan sanda ta yi nasarar bude wuta ga yan bindigar kuma uku sun sheka lahira yayin da aka kai su asibiti bayan samun raunuka
  • A watan Satumba da ya wuce miyagun yan bindigar sun yi yunkurin sace matar dan majalisar amma ba su samu nasarar mugun aikin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Delta - Rundunar yan sanda a jihar Delta ta hallaka wasu yan bindiga da suka yi yunkurin sace matar dan majalisar jiha.

Rundunar yan sanda ta samu kwato muggan makamai daga wajen yan bindigar bayan samun nasara a kansu.

Kara karanta wannan

An cafke matashin da ya sassara dan banga har lahira, ya yi masa sata

Yan sanda
An kashe yan bindiga a Delta. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa yan bindigar da aka kashe din sun mutu ne bayan an kaisu asibiti.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka so sace matar dan majalisa

A ranar 2 ga watan Satumban da ya wuce yan bindiga suka yi yunkurin sace matar dan majalisar a garin Warri.

A lokacin yan bindigar sun yi nasarar kashe yan sanda biyu da matukin motar matar amma ita ta tsira da ranta.

An kashe miyagun yan bindiga a Delta

A ranar Lahadi da ta wuce ne yan sanda suka hango motar yan bindigar da suka kai hari kan matar dan majalisar kuma nan take aka fara musayar wuta bayan yan ta'addar sun fara harbinsu.

Biyo bayan kazamin fada da suka yi ne yan sanda suka samu nasarar kashe uku daga cikin miyagun.

Yadda aka kashe yan bindiga a Delta

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun fatattaki masu sallar juma'a a wasu masallatai a Katsina

Rundunar yan sanda ta bayyana cewa a lokacin da aka fafata da yan ta'addar miyagin sun samu raunuka kuma sun mutu a asibiti.

Haka zalika rundunar ta bayyana cewa ta kwato bindigogi kirar AK47 guda uku yayin da wasu yan ta'addar suka gudu da raunuka a jikinsu.

Yan bindiga sun sace mutane a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun yi ta'asa bayan sun kai hari a garin Kachia da ke jihar Kaduna a Arewa maso Yamma.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a cikin dare yayin da suka riƙa harbe-harbe, lamarin da ya firgita mutanen garin, kuma sun sace mutane da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng