Bello Turji Ya yi Karin Bayani kan Neman Sulhu, Ya yi Martani ga Hafsan Tsaro

Bello Turji Ya yi Karin Bayani kan Neman Sulhu, Ya yi Martani ga Hafsan Tsaro

  • Ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi mutane a Arewacin Najeriya, Bello Turji ya sake sabon bidiyo a kan neman kawo karshen ta'addanci
  • Bello Turji ya ce yana so a kawo karshen zubar da jini a Arewacin Najeriya amma ko da wasa ba wai tsoro ba ne ya sanya shi neman sulhun
  • A makon da ya wuce ne dan ta'addar ta fitar da bidiyo yana so a kawo karshen ayyukan yan bindiga a Arewa domin samar da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji ya yi ƙarin bayani kan neman sulhu da ya yi da gwamnati a makon da ya wuce.

Kara karanta wannan

'Ba ni kadai ba ne', Sheikh Gumi ya fadi wadanda ke raka shi wurin yan bindiga

Bello Turji ya bayyana matakin da ya kamata gwamnatin tarayya ta dauka domin kawo karshen yan ta'adda a Arewa.

Bello Turji
Bello Turji ya kara neman sulhu. Hoto: Muhammad Aminu Kabir
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan da Bello Turji ya yi ne a cikin wani bidiyo da M Inuwa MH ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bello Turji ya ce bai tsoron gwamnati

Bayan Bello Turji ya saki bidiyo neman sulhu, yan Najeriya da rundunar tsaro sun ce ɗan ta'addar ya tsorata ne kuma ƙarshensa ya zo.

A cikin sabon bidiyon da ya yi, Bello Turji ya yi martani kan cewa sam ba jin tsoro ne ya sanya shi neman sulhu ba.

Turji ya fadi sharadin kawo zaman lafiya

Dan ta'adda Bello Turji ya bayyana cewa idan ana son zaman lafiya dole a dakatar da yan sa-kai da suke farautar yan bindiga.

Kara karanta wannan

Bayan kashe Halilu Sububu, hafsan tsaro ya fadi halin da Bello Turji yake ciki yanzu

Ƙasurgumin dan bindigar ya ce idan ba ta wannar hanyar ba, to ba lallai a kawo karshensu ba a kasar nan.

Turji ya koka kan yan sa-kai a Zamfara

Bello Turji ya ce yan sa kai da ake kawowa domin yakar su ba su yi karatu ba balle su san yadda za su samar da tsaro.

Dan ta'addar ya yi ikirarin cewa ana ba su horo ne na makonni uku kawai sannan a ce sun kware domin yakar yan ta'adda.

A kan haka ya ce ko gobe gwamna ko shugaban kasa suka sa aka dakatar da su za su ajiye makamai su rungumi zaman lafiya.

Karshen Turji ya zo inji hafsan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa hafsan tsaro na ƙasa Christopher Musa ya sha alwashi kan Bello Turji wanda ya addabi mutanen jihar Zamfara.

Janar Christopher Musa ya bayyana cewa nan da ɗan ƙanƙanin lokaci za a cafke jagoran 'yan ta'addan da ke Arewa ta yammacin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng