Garambawul: Ministar Tinubu Ta Yi Magana kan Yiwuwar Rasa Mukaminta
- Hannatu Musa Musawa ta yi magana kan shirin da shugaba Bola Tinubu ke yi na sauya wasu daga cikin ministocinsa
- Ministar al'adun ta bayyana cewa ba ta damu da batun yin garambawul ba domin ta amince da duk hukuncin da Tinubu zai yanke
- Hannatu ta yi nuni da cewa duk da abin da shugaban ƙasan ke shirin yi, zai yi ne domin cimma manufofinsa kan ƴan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministar al’adu da tattalin arziƙin fikira, Hannatu Musawa, ta yi magana kan shirin garambawul da shugaba Bola Tinubu yake yi wa majalisar ministocinsa.
Hannatu Musa Musawa ta ce ba ta damu da shirin yin sauyin da shugaban ƙasan yake son yi a majalisar ministocin ba.
Ministar ta bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels tv a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ministar ta ce kan garambawul ɗin Tinubu?
Da aka tambaye ta ko ta damu cewa shugaban ƙasa zai sauke ta daga muƙaminta saboda cece-kucen da ke tattare da ita, ta ce ko kaɗan ba ta damu ba.
"Ba na jin akwai cece-kuce dangane da ni. Ba na jin akwai cece-kuce dangane da ofishina. Abin da zan iya gaya muku shi ne na yi wa shugaban ƙasa yaƙin neman zaɓe kuma na amince da hukuncinsa."
"Abin da na sani game da shugaban ƙasa shi ne yana da buri da manufar ganin ya mayar da Najeriya ta fi yadda ya same ta. Mutum ne mai jarumtaka. A matsayinka na jagora, dole ne ka ɗauki matakan da suka dace."
Saboda haka ban damu ba domin na san Shugaba Tinubu ya na son abin da ya fi dacewa da ƙasar nan kuma duk abin da zai yi dangane da garambawul ko akasin haka kan ministocinsa zai yi ne domin cimma manufofinsa kan ƴan Najeriya."
- Hannatu Musa Musawa
Tinubu ya yiwa ƴan Najeriya albishir
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ce lokaci na zuwa da ƴan Najeriya za su yaba kan yadda gwamnatinsa ta ɗauki matakai masu tsauri.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa matakan da ya ɗauka domin farfaɗo da tattalin arziƙi za su haifar da ɗa mai ido ga ƴan ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng