Tsohon Gwamnan PDP Ya Fadi Hanyar da Za a Ceto Najeriya
- Tsohon gwamnan jihar Sokoto ya koka kan halin ƙunci da tsadar rayuwar da ake fama da shi a ƙasar nan a halin yanzu
- Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya buƙaci shugabanni da su haɗa kai waje ɗaya domin ceto ƙasar nan daga halin da ta tsinci kanta a ciki
- Tambuwal ya yi wannan kiran ne bayan kammala taron jam'iyyar PDP na jihar Sokoto wanda aka gudanar a ranar Asabar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya yi magana kan halin da ƙasar nan ke ciki.
Aminu Waziri Tambuwal ya buƙaci shugabanni da su haɗa kai domin ceto Najeriya daga halin da ta tsinci kanta a ciki.
Tsohon gwamnan na Sokoto ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi bayan kammala taron jam’iyyar PDP na jihar Sokoto a yammacin ranar Asabar, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace shawara Tambuwal ya ba da?
Aminu Tambuwal ya jaddada cewa ƙasar nan na dab da rugujewa saboda munanan manufofin tattalin arziƙi da suka jefa mutane cikin matsanancin talauci, wanda hakan ya sa mutane da dama ba su iya samun abinci.
Ya kwatanta halin da Najeriya ke ciki da kasancewa rai a hannun Allah, kuma ya nuna matuƙar damuwa game da rashin tsaro, matsanancin talauci, da taɓarɓarewar tattalin arziƙi da ke addabar ƙasar nan.
Tambuwal ya yi kira da a haɗa kai a tsakanin shugabanni, musamman waɗanda ba su gamsu da yadda ake gudanar da mulki a yanzu ba.
"Dole ne mu yi aiki tare domin tabbatar da cewa da yardar Allah, ta hanyar tsarin dimokuradiyya, mun ceto ƙasar nan a 2027."
- Aminu Waziri Tambuwal
Tambuwal ya gargaɗi Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya ja kunnen ministocinsa da waɗanda ya naɗa muƙamai kan sukar magabacinsa, Muhammadu Buhari.
Aminu Tambuwal ya bayar da hujjar cewa Tinubu ba zai iya raba kansa da gazawar gwamnatin Buhari ba, don haka ya kamata ya daina kukan ya gaji tattalin arziƙin da ya taɓarɓare.
Asali: Legit.ng