Da Alamu Fetur Zai Sauka bayan Karyewar Farashi a Kasuwar Duniya, an Gano Dalili
- Kungiyar manyan dilalan mai a Najeriya ta MEMAN ta sanar da yiwuwar faduwar farashin mai a kasar a yan kwanakin nan
- Kungiyar ta ce farashin danyen mai ya sauka daga $73.67 zuwa $72.45 wanda ya yi matukar tasiri wurin karya farashin
- Dillalan suka ce hakan bai rasa nasaba da tashin farashin Naira idan aka kwatanta da dala a karshen watan Satumbar 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Akwai alamun farashin mai zai iya yin kasa bayan farfadowar darajar Naira.
Manyan dillalan mai a Najeriya sun tabbatar da cewa na samu faduwar farashin yayin shigo da man daga ketare.
Dillalan mai sun yi magana kan farashi
Kungiyar manyan dillalan man a Najeriya (MEMAN) ta tabbatar da haka a cikin wani rahita da Legit ta bibiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farashin ya ragu daga N981 kan kowane lita a watan Satumbar 2024 zuwa N945.63 zuwa karshen watan.
Dillalan man sun alakanta faduwar farashin kan farfadowar darajar Naira a yan kwanakin nan wanda ya yi tasiri.
Rahoton ya tabbatar da cewa farashin dala ya fadi daga N1,166 zuwa N1,586 a karshen watan Satumbar 2027 da ta gabata.
Manyan yan kasuwa sun fadi farashin danyen mai
Har ila yau, MEMAN ta tabbatar da cewa farashin danyen mai a kasuwar duniya ya fadi $73.67 zuwa $72.45 a ranar 30 ga watan Satumbar 2024.
Wanann na zuwa ne bayan faduwar farashin daga N1,130 a watan Yulin 2024 zuwa N981 wanda hakan ya rage tsadar man a wasu wurare.
Manyan yan kasuwa sun magantu kan farashin mai
Kun ji cewa manyan ‘yan kasuwa sun bayar da rahoton raguwar kudin sauke mai a kasar nan, wanda hakan na iya haifar da faduwar farashin fetur.
A cewar ‘yan kasuwar, kudin sauke mai ya ragu daga N1,300 zuwa N981 kan kowace lita, wanda a ke gani zai shafi farashin man fetur.
Yan kasuwar sun kuma tabbatar da shigo da kusan lita miliyan 141 na man fetur daga kasashen waje ta tasoshin ruwa guda uku.
Asali: Legit.ng