'Yar Kasar Canada Ta Shiga Matsala a Najeriya, NDLEA Ta Cafke Kwayoyin N9bn

'Yar Kasar Canada Ta Shiga Matsala a Najeriya, NDLEA Ta Cafke Kwayoyin N9bn

  • Hukumar NDLEA ta cafke wata ‘yar kasar Canada mai suna Adrienne Munju a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas
  • NDLEA ta ce an kama matar ne a ranar Alhamis, 3 ga Oktoba saboda shigo da kunshi sama da 70 na tabar wiwin ‘Canadian Loud’
  • Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya sanar da kamen a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi tare da yin karin bayani kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Jami’an hukumar NDLEA sun cafke wata ‘yar kasar Canada mai shekaru 41, Adrienne Munju a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.

An kama wadda ake zargin ne a lokacin da ake binciken fasinjojin jirgin KLM daga kasar Canada a tasha ta 1 da ke filin jirgin saman Legas a ranar 3 ga Oktoba, 2024.

Kara karanta wannan

Bayan kashe Halilu Sububu, hafsan tsaro ya fadi halin da Bello Turji yake ciki yanzu

NDLEA ta yi magana kan cafke wata 'yar Canada a filin jirgin saman Legas
NDLEA ta cafke wata 'yar Canada kan shigo da kwayoyi Najeriya. Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

NDLEA ta cafke 'yar Canada a Legas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar NDLEA ta kama Adrienne Munju saboda shigo da wani kaso mai yawa na nau'in tabar wiwi da ake kira 'Canadian Loud' inji rahoton The Punch.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya fitar ranar Lahadi ta ce wannan ne karon farko da Adrienne Munju ta shigo Najeriya.

Femi Babafemi ya ce a lokacin da ake binciken jakunkunan Adreienne guda uku, an gano kunshi 74 na miyagun kwayoyi da nauyinsu ya kai kilogiram 35.20.

'Yar Canada ta shigo da miyagun kwayoyi

Channels TV ta rahoto sanarwar NDLEA ta ce:

"Adrienne Munju ta shaida cewa an ba ta kwangilar shigo da miyagun kwayoyin Legas ne a wani dandalin yanar gizo inda aka ce za a biyata dalar Canada 10,000.
"Ta ce ta karbi wannan kwangilar ne saboda tana bukatar kudin ne domin ci gaba da biyan kudaden karatun digirinta na biyu a wata makarantar Canada."

Kara karanta wannan

Iran vs Isra'ila: Gwamnati ta aika sakon gaggawa ga 'yan Najeriya mazauna Lebanon

Sanarwar ta ce an kuma kama kwayoyin Tramadol, Tramaking Quick Action Tramadol, Tamol-X, Royal Tapentadol da Carisoprodol guda 13,298,000.

Haka zalika an samu kwalebe 338,253 na Codeine. An ce kudaden miyagun kwayoyin sun kai N9,017,771,000 a tashar ruwa ta Onne da ke Fatakwal, jihar Ribas.

NDLEA ta kama ruɓaɓɓun abinci, magani

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar NDLEA ta ce ta kai samame kasuwannin Maiduguri domin bincike kan abinci da magani da suke sayarwa bayan samun korafe-korafe.

NDLEA ta ce jami'anta sun kama abinci da magunguna da suka ruɓe na makudan kudi sama da Naira biliyan biyar wadanda kuma ake sayar da su bayan ambaliyar ruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.