Fargabar Barkewar Ambaliya: Gwamnati Ta Aika Sakon Gaggawa ga Mazauna Jihar Kwara
- An samu rahoton afkuwar ambaliyar ruwa a wasu yankuna na jihar Kwara yayin da aka kwashe kusan kwanaki biyar ana zabga ruwan sama
- Gwamnatin Kwara ta aika sakon gaggawa ga al'ummar jihar da ke zaune a yankunan tekuna da su koma kan tudu domin kare rayukansu
- A yayin da gwamnatin ta jaddada cewa ta dauki matakan ba da kariya daga ambaliyar ta kuma shawarci mutane su kiyaye dokokin SEMA
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - An shiga fargaba a Kwara da ke Arewa maso tsakiyar Najeriya yayin da ake ci gaba da zubga ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihar.
Sakamakon ruwan saman da ya tsananta, gwamnatin jihar Kwara ta aika sakon gaggawa ga mazauna yankunan tekuna da su koma garuruwan tudu.
Shawarar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishiniyar muhalli ta jihar, Nafisat Buge ta fitar a ranar Lahadi inji rahoton The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana fargabar ambaliya a Kwara
Nafisat Buge ta ce an fitar da sanarwar ne domin gargadar mazauna yankunan da ke kusa da takuna akan barazanar ambaliya da ke iya afkuwa.
Jihar Kwara dai na shan ruwan sama a tsakanin Laraba zuwa Lahadi, lamarin da ya kai ga samun rahoton ambaliyar ruwa da a wasu yankunan jihar.
An samu rahoton ambaliyar a yankin kogin Asa da ke titin Unity, Taiwo Isale, da Isale Koko a yankin Ilorin ta kudu da Ilorin ta gabas da ke a jihar.
Gwamnati ta aika sako ga 'yan Kwara
A cewar sanarwar da Nafisat Buge ta fitar:
"Gwamnatin jihar na kira ga mazauna jihar Kwara da su kwantar da hankulansu yayin da ake ci gaba da nazarin yanayin saukar ruwan saman da kuma rahoton ambaliya a wasu yankuna."
Ta ce gwamnatin AbdulRahman AbdulRazaq ta damu matuka da rahotannin da ake samu na ambaliyar ruwa kuma tana daukar matakan tabbatar da tsaron jama'a.
Domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a, kwamishiniyar ta ce:
"Gwamnati na bukatar mazauna yankunan takuna su koma kan tudu, a kauracewa zirga zirga lokacin ruwa sannan a bi matakan kariya da SEMA ta bayar."
Ambaliya ta yi barna a Kwara
Tun da fari, mun ruwaito cewa an samu afkuwar ambaliyar ruwa a garin Bode Sa'adu, hedikwatar karamar hukumar Moro ta jihar Kwara inda kadarori na miliyoyin Naira suka lalace.
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya kai ziyara garin Bode Sa'adu inda ya jajantawa al'umma da kuma duba barnar da afkuwa bayan ruwan sama na kwanaki hudu.
Asali: Legit.ng