"Wasu ba Su Jin Dadi": Shehu Sani kan Kokarin Matawalle a Yaki da Ta'addanci
- Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yabawa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle kan yaki da ta'addanci
- Shehu Sani ya kuma bukaci al'umma da su bar sukar Matawalle da Nuhu Ribadu inda ya ce hakan na kawo cikas a yaki da ta'addanci
- Sanatan ya bukaci al'umma da su cigaba da ba da goyon baya domin ganin an kawo karshen rikicin ba sukar juna ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya magantu kan matsalar ta'addanci a Arewa.
Shehu Sani ya ce abin takaici ne yadda ake sukar ƙaramin Ministan tsaro, Bello Matawalle da Nuhu Ribadu kan lamarin.

Asali: Facebook
Shehu Sani ya caccaki masu sukar Matawalle
Tsohon sanatan ya bayyana haka yayin ganawa da yan jaridu a jihar Kaduna, kamar yadda Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan ya ce sukar Matawalle da Ribadu yana kawo tsaiko a kokarin dakile hare-haren yan bindiga.
Shehu Sani ya ce tabbas a yanzu ana kokari musamman a yaki da ta'addanci inda ya tabbatar da cewa an fara yin galaba a kansu.
Ta'addanci: Shehu Sani ya kan masu kawo cikas
Ya nuna damuwa kan yadda wasu tsiraru ba su jin dadin yadda ake hallaka kasurguman yan bindiga a yankin.
"Yanzu da ake samun nasara kan yan bindiga, ya kamata Janar Christopher Musa da Bello Matawalle da Nuhu Ribadu su mayar da hankali sosai kada su bari a kawar musu da hankali."
"Duk wanda ke burin a kawo karshen wadannan miyagu dole ya ba da goyon baya wurin dakile matsalar madadin suka da bai da amfani."

Kara karanta wannan
"Abin da ake tsoro kenan": Sheikh Gumi kan mummunan akida da yan bindiga suka dauko
- Shehu Sani
2027: Shehu Sani ya roki yan Arewa
Kun ji cewa Shehu Sani ya bayyana cewa kamata ya yi Arewa ta hakura ta bar ƴan Kudu su ci gaba da mulkin Najeriya a babban zaɓen 2027.
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya ya ce daga nan kuma Arewa za ta samu cikakkiyar damar samar da shugaban ƙasa a 2031.
Ya ƙara da cewa Bola Tinubu ya cancanci ya kara samun goyon bayan ƴan Arewa saboda abin da ya yi masu lokacin zaben 2015.
Asali: Legit.ng