Yaron Sanusi II Ya Amsa Nuhu Ribadu da NSA Ya Kira Aminu Ado Bayero Sarkin Kano

Yaron Sanusi II Ya Amsa Nuhu Ribadu da NSA Ya Kira Aminu Ado Bayero Sarkin Kano

  • An ji Malam Nuhu Ribadu a wani gajeren bidiyo ya na bayyana Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano
  • Tun tuni gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta tsige sarakunan da Abdullahi Ganduje ya nada, ta rushe masarautunsu
  • Duk da an maido Muhammadu Sanusi II, Ribadu ya nuna Aminu Ado ya sani a matsayin sarki har gobe a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Nuhu Ribadu ya jawo abin surutu yayin da aka ji ya kira Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano.

Kalaman Malam Nuhu Ribadu sun tada kura ne ganin shi ne mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkar tsaro.

Ashraf Sanusi Ado
Ashraf Sanusi ya yi watsi da zanen Nuhu Ribadu kan sarautar Kano Hoto: @Adam_L_Sanusi/@uaaliyu
Asali: Twitter

Ashraf Sanusi, Ribadu da sarautar Kano

Ashraf Lamido Sanusi wanda mahaifinsa ya dawo kan karaga ya yi magana a shafin X bayan maganar Nuhu Ribadu.

Kara karanta wannan

Ganduje ya bayyana wanda ya ceci jam’iyyar APC daga asarar Naira biliyan 1.5

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam Ashraf Sanusi ya gagara yin shiru a lokacin da ya ji magoya bayan Aminu Ado Bayero sun samu kwarin guiwa.

An rahoto cewa Abba Kabir Yusuf ya maido Muhammadu Sanusi II kan sarauta da ya sauke sarakunan jihar Kano.

A wani taro da aka yi a Abuja, sai aka ji Ribadu ya na kara karfafar Aminu Ado wanda ake rikicin sarautar Kano da shi.

Tasirin Nuhu Ribadu a sarautar Kano

Da yake maida martani a ranar Juma’a, Ashraf Sanusi II ya nuna cewa matsayar Ribadu ba ta da wani amfani a Kano.

Duk da shi yake rike da sha’anin tsaro a gwamnatin tarayya, tsohon shugaban na EFCC bai da ta-cewa kan sarautar jiha.

"Da zai kasance labari idan ya na da muhimmanci wajen zaben Sarkin Kano."

Kara karanta wannan

“An samu tsaro a Najeriya”: Ribadu ya fadi bambancin gwamnatin Tinubu da Buhari

- Ashraf Lamido Sanusi

A doka, sha’anin masarauta ya rataya ne kan gwamnatin jiha da majalisar nada sarakuna.

Martanin mutane kan rikicin Sanusi II v Aminu Ado

Da jin sabon angon ya yi wannan magana, mutane da ake amfani da dandalin su ka fara tofa albarkacin bakinsu a Twitter.

Wani mai suna Mai Fulawa ya ce:

“Ado Bayero ne sarkin Kano har yanzu. Allah ya karawa tsohon Sarki Sanusi lafiya.”

Shi kuwa @Ibrahym_Jnr yake cewa duk sarkin da bai da iko a kasarsa bai cika mai martaba ba.

Wani Musa Ribadu kuwa ya ce Alhaji Aminu Ado ne Sarkin Kano.

Sulaiman Mustapha Adam ya ce shi so ya yi Sanusi II ya koma gwamnan bankin CBN ba ya dawo gidan dabo ba.

A cewar @Oyerinde, Sanusi II ba shi ba ne Sarki domin ba a bi doka wajen tunbuke Aminu Ado Bayero ba.

An taso Ashraf Sanusi a gaba

Kara karanta wannan

'Ya lalata komai,' Kwankwaso ya tono 'barnar' da Ganduje ya yi a Kano

Kwanaki aka samu labari 'dan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, Ashraf Sanusi ya gamu da 'yan adawarsu a shafin X.

An yi masa ca bayan ya yi martani kan hukuncin da kotu ta yi inda ake tunanin an soke nadin mahaifinsa da aka sake yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng