Wike: Sunayen Manyan 'Yan Siyasa 60 da Za Su Iya Rasa Filayensu a Birnin Abuja
Abuja - Hukumar FCTA za ta sa kafar wando daya da wasu daidaikun mutane da kamfanoni a babban birnin tarayya Abuja.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
FCTA ta na barazanar karbe takardun shaidar mallakar wasu filaye da ke unguwar Maitama idan ba su biya bashin kudinsu ba.
FCTA za ta iya raba mutane da filayensu
Rahoton Punch ya bayyana cewa an yi wa masu filayen barazana a ranar Juma’a cewa za su iya rasa kasarsu idan har suka yi sake.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da ya sa ake so a biya kudin shi ne domin gwamnati ta cigaba da ayyukan more rayuwa a shiyyar Maitama II (A10) a birnin Abuja.
Legit Hausa ta bibiyi jerin da Premium Times ta kawo, ta tattaro sunayen wadanda abin ya shafa a karkashin jagorancin Nyesom Wike.
‘Ya ‘yan manyan da ke cikin matsala a Abuja
1. Yusuf Buhari
2. Zahra Buhari
Manyan gwamnati da za su iya rasa filaye
3. Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen
4. Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume
5. Shugaban fadar ma’aikatan gidan gwamnati, Femi Gbajabiamila
Tsofaffin shugabannin majalisa
6. Ameh Ebute
7. Bukola Saraki
8. Yakubu Dogara
9. Ovie Omo-Agege
Ministocin gwamnati na cikin matsala a Abuja
10. Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo
11. Ministan wasanni, John Eno
12. Ministan noma, Abubakar Kyari
Tsofaffin sanatoci, gwamnoni da ministoci
13. Chris Nigige
14. Theodore Orji
15. Rochas Okorocha
16. Ibikunle Amosun
17. Tanko Al-Makura
18. Joshua Dariye
19. Gabriel Suswam
20. Ibrahim Shekarau
21. Okezie Ikpeazu
22. Jonah Jang
23. Adamu Muazu
24. Marigayi Bukar Abba Ibrahim
25. Dino Melaye
26. Kabiru Marafa
27. Stella Oduah
28. Ben Bruce
29. David Umaru
30. Biodun Olujimi
31. Andy Uba
32. Emmanuel Bwacha
33. Kabiru Gaya
34. Peter Nwaoboshi
35. Philip Aduda
36. Binta Garba
37. Teslim Folarin
38. Darlington Nwokocha
39. Smart Adeyemi
40. Ben Obi
41. Abdullahi Adamu
FCTA za ta iya karbe filayen Sanatoci masu-ci
42. Danjuma Goje
43. Saliu Mustapha
44. Sunday Karimi
45. Ali Ndume
46. Osita Izunaso
47. Seriake Dickson
48. Chukwuka Utazi
49. Oker Jev
Tsofaffi da ‘yan majalisar wakilai masu-ci
50. Olumide Osoba
51. Nicholas Ossai
52. Wole Oke
53. Julius Ihonvbere
54. Khadijat Ibrahim
55. Lynda Ikpeazu
56. Obinna Chidoka
57. Beni Lar
58. Leo Ogor
59. Timothy Golu
60. Edward Pwajok
'Yan siyasar da za su iya yakar Tinubu
A wani rahoto, an ji cewa akwai wasu ’yan siyasar Kudancin Najeriya da ka iya neman takawa Bola Tinubu burki a zaben 2027.
Wasu ’yan siyasar kudancin kasar nan na iya kalubalantar shugaba Bola Tinubu. Daga cikinsu akwai Peter Obi da Nyesom Wike.
Asali: Legit.ng