Gwamna a Arewa Ya Dakatar da Basarake da Tsohon Gwamnan Jihar Ya Nada, an Fadi Dalili

Gwamna a Arewa Ya Dakatar da Basarake da Tsohon Gwamnan Jihar Ya Nada, an Fadi Dalili

  • An kalubalanci gwamna kan dakatar da basarake ba bisa ka'ida ba bayan darewa sarauta fiye da shekara daya
  • Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau shi ya umarci basaraken ya sauka daga mukaminsa domin gudanar da bincike
  • Sai dai kungiyar cigaban masarautar da ake kira BACODA ta tabbatar da cewa babu matsala a tsarin nadin Sarkin da aka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Dakatar da basarake da Gwamna Caleb Mutfwang a jihar Plateau ya yi na neman zama wani abu daban.

Kungiyar cigaban masarautar Bashar (BACODA) ta bukaci adalci bayan dakatar da basaraken babu dalili.

An kalubalanci gwamna kan dakatar da basarake a Plateau
Masarauta ta kalubalanci Gwamna Caleb Mutfwang kan dakatar da basarake a Plateau. Hoto: Caleb Mutfwang.
Asali: Twitter

Plateau: Kungiya ta kalubanci gwamna kan basarake

Kara karanta wannan

Kungiya ta fadawa Tinubu ribar da zai samu idan ya sasanta rikicin masarautar Kano

Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamna Caleb Mutfwang ya dakatar da basaraken a yankin Bashar, Alhaji Abdullahi Idris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren kungiyar kuma Sarkin Malaman Bashar, Alhaji Yunusa Aliyu ya ce sun kadu da jin cewa an bukaci basaraken a jihar ya ajiye sarautar domin gudanar da bincike.

Alhaji Yunusa ya ce an bi dukan ka'idoji wurin nadin Sarkin da aka yi a 2022 inda aka turawa gwamnati yadda aka yi gudanar da lamarin.

Yadda aka gudanar da nadin sarautar a Plateau

"Muna da bayanan yadda aka gudanar da nadin sarautar wanda duk masu ruwa da tsaki sun halarta."
"An bi dukan tsarin da ya kamata har ma da daukar bidiyo da aka turawa gwamnati a 2022.
"Rahoton ya nuna jerin sunayen masu neman sarauta da masu nadinta da kuma wakilai daga kwamitin sarakunan gargajiya na jihar Plateau."

Kara karanta wannan

Majalisa ta yi amai ta lashe kan dakatar da mambobinta, ta fadi dalili

- Yunusa Aliyu

Yunusa Aliyu ya ce babu wani wanda ya kalubalanci yadda aka gudanar da nadin a wancan lokaci inda ya ce a hukumance basaraken Bashar ya karbi takardar nadin muƙamin a watan Janairun 2023.

Daga bisani gwamnan jihar a wancan lokaci ya tabbatar da nadinsa a matsayin Sarki a ranar 23 ga watan Fabrairun 2023.

Dattawa sun kalubalanci Gwamna kan sarauta

Kun ji cewa Zanga-zanga ta barke yayin da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya tabbatar da nadin sabon sarki.

Dattawa da shugabannin yankin Okpella a jihar sun yi fatali na nadin Lukman Akemokhue a matsayin sarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.