‘Dan Takara Ya Ceci Yaron Talaka, Ya Biya Masa Kudin Karatu Zuwa Jami’a a Katsina

‘Dan Takara Ya Ceci Yaron Talaka, Ya Biya Masa Kudin Karatu Zuwa Jami’a a Katsina

  • Isah Miqdad ya dage wajen ganin mutanen karamar hukumarsa musamman marasa karfi sun samu ilmin zamani
  • ‘Dan takaran na APC a karamar hukumar Katsina a zaben 2024 ya na cigaba da taimakawa bayin Allah a harkar ilmi
  • Bayan rabon kayan karatu da rubutu da ya yi, Malam Isah Miqdad ya dauki nauyin karatun wani har zuwa jami’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Katsina - Isah Miqdad ya taimaka wani yaro ta yadda zai samu rayuwa mai kyau domin kuwa ya dauki nauyin karatun bokonsa.

Isah Miqdad shi ne mai taimakawa gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda a harkokin kafofin sadarwa na zamani tun a shekarar 2023.

Isah Miqdad
Isah Miqdad zai biyawa yaro karatu zuwa jami'a a Katsina Hoto: @Miqdad_Jnr
Asali: Twitter

Isah Miqdad: 'Dan takara ya taimakawa yaro

Kara karanta wannan

Ganduje ya bayyana wanda ya ceci jam’iyyar APC daga asarar Naira biliyan 1.5

Hadimin gwamnan na Katsina wanda ya ke takarar shugaban karamar hukuma ya bayyana wannan a shafinsa na X (Twitter).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashin ya bayyana cewa ya dauki nauyin Muhammad Salisu, wani yaro da ya hakura da karatun sakandare a kauyen Kambarawa.

A sanadiyyar Isah Miqdad, Muhammad Salisu zai yi karatu har ya gama sakandare kuma ya wuce jami’a ba tare da biyan kudi ba.

Burin 'dan takaran APC a Katsina

‘Dan takaran na APC a zaben karamar hukumar Katsina ya ce wannan hobbasa da ya yi duk ya na cikin burinsa na tallafawa matasa.

Miqdad yake cewa ya na son ganin marasa galihu sun samu ilmi mai nagarta ta yadda rayuwarsu za ta iya yin kyawu nan gaba.

Yara 175 sun amfana da shirin Isah Miqdad

A wani bayani da ya yi a shafin nasa, ‘dan siyasar ya ce ya dauki nauyin dalibai 175 da ke karatun sakandare a karamar hukumarsa.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi ta'aziyyar yan maulidi 150 da ake fargabar sun mutu a hadarin jirgi

An zabo yaran ne daga makarantu 21 da ke mazabu 12 a karamar hukumar Katsina.

Lamarin bai tsaya nan ba, mai ba gwamnan na Katsina shawara ya raba kayan karatu jaka, hijabai da sauransu ga dalibai har 280.

Duk an yi wannan ne cikin makonni uku da ‘dan takaran ya kaddamar da wani tsarin karatu da ya fito da shi domin marasa hali.

'Yan kasuwa za su samu N1m a Katsina

Kananun 'yan kasuwa a jihar Katsina za su samu rancen kudi Naira miliyan guda kamar yadda aka samu labari kwanakin baya.

Gwamnatin Katsina da hukumar SMEDAN ne suka yi yarjejeniyar kan bayar da tallafin kamar yadda Mal. Isah Miqdad ya sanar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng