Ganduje Ya Bayyana Wanda Ya Ceci Jam’iyyar APC daga Asarar Naira Biliyan 1.5

Ganduje Ya Bayyana Wanda Ya Ceci Jam’iyyar APC daga Asarar Naira Biliyan 1.5

  • Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa Abdulkareem Abubakar Kana wajen bikin da aka shirya domin karrama shi
  • Shugaban APC na kasa ya ce mai ba jam’iyyar shawara a kan shari’a ya taka rawar gani wajen hana su rasa N1.5bn
  • Farfesa Abdulkareem Abubakar Kana wanda ya na cikin majalisar NWC a APC ya samu karin matsayi ne zuwa SAN

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Shugaban APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje ya ba da labarin wasu abubuwan da su ka faru da jam’iyya mai mulki.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa an yi hukunci a kotu inda aka nemi a rike kudin APC har N1.5bn da ke asusun banki.

Ganduje
Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje Hoto: Abubakar Aminu Ibrahim
Asali: Facebook

Lauyan APC na kasa ya zama SAN

Kara karanta wannan

'An kai mutumin da ya nemi Tinubu ya sauka daga mulki asibitin masu tabin hankali

An fahimci wannan daga rahoton Daily Trust da ya ce shugaban APC ya yi magana wajen karrama Abdulkareem Abubakar Kana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An shirya taro na musamman domin taya Farfesa Abdulkareem Abubakar Kana murnar samun matsayin SAN a aikinsa na lauya.

Ganduje ya yabi Kana, Fagge

Abdulkareem Kana shi ne mai ba jam’iyyar APC shawara a kan harkokin shari’a, ya na cikin wadanda aka zaba su zama SAN a bana.

Leadership ta ce Abdul Adamu Fagge wanda Abdullahi Ganduje ya ce ya ba APC gudumuwa sosai, ya shiga sahun manyan lauyoyi.

Rikicin jam'iyyar APC da lauyoyin a kotu

Akwai lokutan da APC ba ta biya lauyoyinta kudin aiki ba musamman lokacin zabe, saboda haka aka shigar da karar jam’iyyar a kotu.

A 2021 wata kotu da ke garin Uyo a Akwa Ibom ta ce a rufe asusun jam'iyyar APC saboda gaza biyan lauyoyinta hakkokinsu na N30m.

Kara karanta wannan

Jiga jigan NNPP a Kano da Arewa da suka tsallake Kwankwaso zuwa APC

Louis Akanimo da Fidel Albert sun wakilci jam’iyyar APC a kotun sauraron korafin zaben 2015 amma su ka koka cewa ba a sallame su ba.

Ta ya Farfesa Abdulkareem Kana ya ceci APC?

Ganduje wanda ya samu wakilcin Hon. Ali Bukar Dalori ya ce Farfesa Kana ya ceci jam’iyyar a lokacin, ya hana APC yin asarar miliyoyi.

A wani lokacin kuma, Dalori ya ce Farfesan ya shiga ya fita domin ceton APC daga biyan N92m duk a sanadiyyar hukuncin wata kotu.

Shugaban PDP ya caccaki APC, LP & NNPP

Kwanaki labari ya zo cewa Ambasada Umar Iliya Damagum ya ce an kawo APC, NNPP da kuma LP ne domin cin zabe kurum a Najeriya.

Idan ana zancen cikakkiyar jam’iyya, shugaban PDP na kasa ya ce duk Afrika ba su da sa’a duk da PDP ta rasa mulki da rinjaye tun a 2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng