Cikakken Jerin Abubuwa 63 da Gwamnatin Tinubu Ta Cirewa Harajin VAT
- Akwai wasu kaya da yawa da gwamnatin tarayya ta yi doka domin daina karbar harajin VAT a kan su a Najeriya
- Wadannan abubuwan sun hada da na’urori da kayan aikin CNG da LPG da motoci masu amfani da wutar lantarki
- An yi wannan ne bayan aikin da Taiwo Oyedele ya yi a matsayin shugaban kwamitin gyara sha’anin haraji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Gwamnatin tarayya ta sanar da cire harajin VAT daga wasu kayayyaki da nufin kawo saukin kuncin rayuwa da ake ciki.
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta dauki wannan mataki ne a sakamakon kudiri da aka kawo da zai canza tsari na karbar haraji.
An cire harajin VAT a abubuwa 63
A wani rahoto, jaridar Punch ta tattaro jerin abubuwan da aka janye karbar harajin VAT a kan su da nufin kawo saukin farashinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taiwo Oyedele ya yi ruwa ya tsaki wajen ganin na yi wannan a matsayinsa na shugaban kwamiti a kan gyaran sha’anin haraji.
Sahara Repoters ta ce tsare-tsaren za su habaka harkar kasuwancin gas da mai a Najeriya.
Jerin abubuwan da aka cirewa VAT
1. Motocin masu amfani da fetur da kuma CNG/LPG
2. Abubuwan hawa masu amfani da LPG da masu aiki da fetur da kuma CNG/LPG
3. Bangarorin manyan motocin CNG da LPG
4. Bangarorin motoci masu aiki da lantarki
5. Motocin lantarki
6. Batiran motocin lantarki
7. Na’urorin cajin motocin lantarki
8. Na’urorin caji da rana na motocin lantarki
9. Na’urar sauya motoci zuwa LPG/CNG
10. Tulun CNG
11. CNG Cascades
12. CNG Dispensers
13. Janaretan gas
14. Manyan motocin CNG (Kananun tirela da sauransu)
15. Bututun Steel
16. Bawul na Steel
17. Bututun SS
18. Tankunan ajiya
19. Regulators
20. Fanfo da komfuresan CNG
Sauran kayan da aka cirewa VAT
21. Steel
22. Pressure Relief Valves
23. Hydraulic press/Rolling machine
24. Heat Treatment Equipment
25. Liquid Level Guage
26. Pumping Housing and Motors
27. Regulator Body
28. Na’urar geji
29. Truck Chassis
30. Na’urar awo
31. Na’urar zuba mai ko gas
32. Na’urorin kariya
33. Injin tafasa ruwa na gas
34. Manyan Gas burners
35. Injin tafasa na gas
36. Injin sukola na gas
37. Tiyon CNG, LP, dsr
38. Kan motocin CNG
39. Na’urar gano yoyon gas
40. Injin AC na gas
41. Na’urar gyara tulun gas
42. Injin Blending skid/unit
43. Odourizing unit
44. Injin Chromatography (GC)
45. Na’urar narka LNG
46. Tashar narka CNG
47. Kayan aikin LNG
48. Na’urorin awo
49. Tankin Cyrogenic da na juya LNG
50. Bututun aikin LNG
51. Kayan lantarki na aikin LNG
52. Sinadaran LNG
53. Karafuna da faifen LNG
54. Biogas Digester
55. Komfureson Biogas
56. Na’urar cire Sulhpur
57. Injin busarwa
58. Kofunan tace Biofuel
59. Kayan aikin matatar Bio-ethanol
60. Tankunan tsimi
61. Sinadaran Biofuel
62. LPG & CNG
63. Gas na motoci
Gwamnati ta hakura da harajin VAT
A kwanaki aka rahoto cewa Gwamnatin tarayya ta dakatar da harajin VAT kan wasu kayayyakin da ake amfani da su a Najeriya.
Ma'aikatar kudi ta kasa ce ta fitar da sanarwa kan lamarin kuma ta ce za a samu sauki da habakar tattali a sanadiyyar hakan.
Asali: Legit.ng