Ba Daraja: Shugaban Karamar Hukuma na Matsala kan Zargin Garkuwa da Kisan Kai

Ba Daraja: Shugaban Karamar Hukuma na Matsala kan Zargin Garkuwa da Kisan Kai

  • An gurfanar da shugaban karamar hukuma mai ci kan zargin garkuwa da mutane da kuma kisan kai
  • Wanda ake zargin, Emmanuel Ajah shi ke jagorantar karamar hukumar Ivo a jihar Ebonyi da ke Kudancin Najeriya
  • Bayan zargin kisan kai da garkuwa da mutane, ana kuma tuhumar Ajah da yin fashi da makami a shekarar 2017

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ebonyi - Kotu a jihar Ebonyi ta yi zama kan shari'ar da ake zargin shugaban karamar hukuma da fashi da makami.

Ana kuma zargin shugaban karamar hukumar Ivo da ke jihar, Emmanuel Ajah da garkuwa da mutane da kuma kisan kai.

Kara karanta wannan

Shugaban Izala ya rasu, al'ummar Musulmi sun shiga jimami

An tsare shugaban karamar hukuma kan zargin garkuwa da mutane
Shugaban karamar hukuma a jihar Ebonyi, Emmanuel Ajah ya shiga matsala kan zargin garkuwa da kisan kai. Hoto: Legit.
Asali: Original

Ana zargin ciyaman da garkuwa da mutane

Premium Times ta ruwaito cewa ana zargin Ajah da wasu mutane takwas da zargin yi wa Pauline Osita fashi da makami.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin sun yi wa Osita fashi ne na N2m da wasu kayayyakinta masu muhimmanci tun a watan Janairun 2017.

Har ila yau, akwai zargin yin garkuwa da Catherine Okorie kafin daga bisani su hallaka ta a watan Janairun 2017.

Daga cikin wadanda ake zargin akwai Chibuike Okereke da Mathew Ogbudike da Ezenwa Nwaforda Okoro Ugochukwu.

Sai kuma Kelechukwu Azubike da John Nwankwor da Chigozie Okereke da kuma Obichi Uzoigwe.

Matakin da alkalin kotun ta dauka kan lamarin

Alkalin kotun, Mai Shari'a, Elvis Ngene shi ya jagoranci shari'ar a yau Juma'a 4 ga watan Oktoban 2024 a birnin Abakaliki da ke jihar.

Bayan sauraran bahasi daga duka bangarorin, Ngene ya dage shari'ar zuwa ranar 21 ga watan Nuwambar 2024 da ke tafe.

Kara karanta wannan

An kara gano gawarwakin 'yan maulidi da jirginsu ya kife a Neja

An kama hatsabibin boka a Ebonyi

Kun ji cewa asirin wani boka mai maganin gargajiya ya tonu yayin da aka kama shi dauke da kasusuwan sassan jikin ɗan Adam da dama.

Bokan ya bayyana abin da yake aikatawa da kasusuwan da kuma wanda ya ba shi su daga jihar Ebonyi da ke kudancin Najeriya.

Kakakin yan sanda a jihar Anambara, SP Ikenga Tochukwu ya tabbatar da faruwar lamarin tare da faɗin halin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.