Yan Bindiga Sun Fatattaki Masu Sallar Juma'a a Wasu Masallatai a Katsina
- Wasu miyagun yan bindiga sun farmaki masallata da ke tsakiyar sallar Juma'a a yau dinnan a jihar Katsina
- An kai harin ne a wani masallaci da ke Dan Ali a karamar hukumar Dan Musa lamarin ya sa jama'a firgici
- Zuwa yanzu dai jami'an tsaron sa-kai sun kora yan ta'addan, yayin da su ke jiran dauki daga wajen jami'an tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina - Wasu miyagun yan ta'adda sun kutsa garin Dan-Ali da ke karamar hukumar Dan Musa inda su ka fatattaki masu gudanar da sallar Juma'a.
Yan bindigar sun shiga garin Dan Ali su na harbin kan mai uwa da wabi, wanda ya firgita mutanen garin da masallatan.
A labarin da ya kebanta da jaridar Punch, wani da lamarin ya rutsa da su ya bayyana cewa harbin ya sa dole su ka katse sallar, kowa ya yi ta kansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan sa kai sun kori yan bindiga
Masallatan da yan bindiga su ka auka masu a Katsina sun bayyana cewa jami'an tsaron Katsina na Security Watch Corps ne su ka fatattaki yan ta'addan.
Yan bindigar sun kai hari garin Dan Ali lokacin da ake tsaka da gudanar da sallar Juma'a a yau.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Katsina, ASP Abubakar Sadiq ya shaidawa Legit cewa ana bincike kan harin.
Mazauna Katsina sun nemi agajin jami'an tsaro
Mazauna jihar Katsina, musamman yankunan Dan-Ali, Gwarjo, Dangane, Tudun, Tasha Kadanya da Tasha Biri sun nemi taimakon jami'an tsaro.
Sun bayyana cewa yan ta'adda sun takura masu, inda su ka hana jama'a sakat tare da hana manoma shiga gonakinsu.
Fada ya kaure tsakanin yan bindiga
A wani labarin, kun ji cewa dara ta ci gida yayin da fada ya kaure tsakanin dabar yan bindiga a yankin Dan Ali da ke karamar hukumar Dan Musa a jihar Katsina.
Kazamin rikicin ya sada miyagun yan ta'adda sama da 20 ga mahaliccinsu, ciki har da wasu daga cikin jagororin yan bindigan da su ka hana jama'a zaman lafiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng