“An Samu Tsaro a Najeriya”: Ribadu Ya Fadi Bambancin Gwamnatin Tinubu da Buhari

“An Samu Tsaro a Najeriya”: Ribadu Ya Fadi Bambancin Gwamnatin Tinubu da Buhari

  • Gwamnatin Bola Tinubu ta sake bugun kirji kan yadda ta magance matsalar tsaro a Najeriya, idan aka kwatanta da lokacin Muhammadu Buhari
  • An ga Nuhu Ribadu, mai ba Tinubu shawara kan harkokin tsaro a wani bidiyo ya na mai cewa Najeriya ta samu tsaro kuma ana zaman lafiya
  • Kalaman Ribadu na ci gaba da janyo martani daga ‘yan Najeriya inda wasu ke kalubalantar shi da ya zagaya kasar ba tare da masu kariya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin Bola Tinubu ta yiwa tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari shagube kan tsaro a 2022 da 2023 idan aka kwatanta da kokarin gwamnati a yanzu.

A ranar Ahamis, Nuhu Ribadu, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, ya yi ikirarin cewa a yanzu Najeriya na da tsaro idan aka kwatanta da lokacin gwamnatin Buhari.

Kara karanta wannan

'An kai mutumin da ya nemi Tinubu ya sauka daga mulki asibitin masu tabin hankali

Gwamnatin Tinubu ta sake bugun kirji kan magance matsalar tsaron Najeriya
Ribadu ya yi magana a kan rashin tsaro a karkashin Tinubu idan aka kwatanta da zamanin Buhari. Hoto: @officialABAT, @MBuhari, @NuhuRibadu
Asali: Twitter

Ribadu ya kuranta gwamnatin Tinubu

A bidiyon da The Cable ta wallafa, an ji Nuhu Ribadu na cewa ofisoshin ‘yan sanda a yankin Kudu maso Gabas sun dawo aiki, ‘yan fashi da ‘yan ta’adda a Arewacin kasar sun fara tserewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai ba shugaban kasar shawara ya kara da cewa ba za a taba cin nasara a hare-haren da ake kai wa gidajen yari domin kubutar da 'yan ta'adda da kuma farmakar jiragen kasa ba.

Wasu 'yan Najeriya sun shiga sashen sharhi na faifan bidiyon domin bayyana ra'ayoyinsu kan kalaman nasa.

Tsaro: An yiwa Ribadu martani

Dakta D. Udoh ya kalubalanci mai ba shugaban kasar shawara yana mai cewa:

"To shikenan, ba matsala. Ba zan yi jayayya da kai ba. Kawai ka tuka kanka a mota daga Abuja zuwa Kaduna ba tare da masu kariya ba, daga nan za ka san halin da ake ciki."

Kara karanta wannan

Sanusi II Vs Aminu: Hayaniya ta ɓarke da Nuhu Ribadu ya kira sunan Sarkin Kano a wani taro

Val Mary yayi sharhi da cewa:

"Ya kamata shugaba ya zama abin koyi. Ka nuna wa 'yan Najeriya yadda ake tafiye-tafiye ba tare da jami'an tsaro masu ba ka kariya ba."

Wani mai amfani da @pdauda ya rubuta cewa:

Ya yarda cewa rashin tsaro ya yi kamari a karkashin Buhari, kuma gaskiya ne, amma kuma karya yake yi kamar yadda ya saba, cewar kasar nan ta samu zaman lafiya a yanzu.
Ba za ku iya tuka mota daga Abuja zuwa Lokoja ba ko kuma Lokoja zuwa Abuba ba tare da fuskantar barazanr masu garkuwa da mutane ba."

Kalli bidiyon a kasa:

Ra'ayin Tinubu kan tsaro a mulkin Buhari

A wani labarin, mun ruwaito cewa Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC a zaben 2023 ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ta rage ayyukan ta’addanci a Najeriya.

A fahimtar Tinubu, Buhari ya samu nasararori a yaki da 'yan ta'adda shiyyoyin kasar nan tun daga lokacin da ya karbi mulki a shekarar 2015 zuwa shekaru takwas na mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.