Kano: Abba Ya yiwa Ganduje Gugar Zana yayin Raba Kayan Miliyoyi a Makarantu

Kano: Abba Ya yiwa Ganduje Gugar Zana yayin Raba Kayan Miliyoyi a Makarantu

  • Gwamnatin jihar Kano ta raba kayan karatu na miliyoyin kudi a makarantun gwamnati domin farfaɗo da harkar ilimi
  • Mai girma Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da yin ayyuka domin farfaɗo da darajar ilimi a jihar Kano
  • Gwamnan yake cwa a lokacin Abdullahi Ganduje harkar ilimi ta yi baya sosai saboda haka suke kokarin farfaɗo da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya raba kayan karatu a makarantun jihar Kano yayin da aka fara sabon zangon karatu.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ya dauki matakin ne ganin yadda gwamnatin da ta wuce ta mayar da Kano baya a harkar ilimi.

Kara karanta wannan

Lambar girma: Abba ya kere dukkan gwamnoni, ya zama na 1 a Najeriya

Abba Kabir Yusuf
Abba ya raba kayan karatu a Kano. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan da gwamnan ya yi ne a cikin sakon da daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya yi wa Ganduje gugar zana

Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatin Abdullahi Gabduje ta kawo ci baya sosai a harkar ilimi a jihar Kano.

A karkashin haka ya ce gwamnatinsa za ta yi dukkan mai yiwuwa domin dawo da martabar ilimi da aka zubar a Kano.

Abba ya raba kayan karatu a makarantu

A kokarin farfaɗo da ilimi, Abba Kabir ya raba kwalayen alli 120,000, kwalayen littatafan rubutu 93,600 da rajista guda 199,234.

Haka zalika gwamnan ya raba kwalayen din littafin aiki na musamman guda 97, 600, rubutun sabon taken Najeriya 30,000 da sauransu.

Jawabin Abba wajen raba kayan karatu

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce kayan karatun za su taimaka wajen inganta ilimi sosai a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Ana fama da wahala, gwamna ya rabawa manyan sarakunan Arewa 4 motocin alfarma

Abba Kabir Yusuf ya kara da cewa samar da ilimi mai inganci ne hanyar da za a bi wajen samar da gobe mai kyau ga al'umma.

An ba gwamna Abba lambar girmamawa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu lambar girmamawa inda aka zaɓe shi a matsayin gwamnan gwamnoni.

A bisa zaben Abba Kabir Yusuf da aka yi, hakan na nuni da cewa gwamnan jihar Kano ya sha gaban dukkan gwamnonin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng