Rigima Sabuwa: Gwamna Ya Dakile Shirin 'Yan Sanda Na 'Sace' Kayan Zaben Ciyamomi

Rigima Sabuwa: Gwamna Ya Dakile Shirin 'Yan Sanda Na 'Sace' Kayan Zaben Ciyamomi

  • Gwamna Siminalayi Fubara ya dakile yunkurin wasu da ake zargin ‘yan sanda ne na sace kayayyakin zabe daga ofishin hukumar RSIEC
  • An rahoto cewa wasu 'yan sanda bisa jagorancin wani mataimakin kwamishinan 'yan sandan Ribas ne suka kai farmaki ofishin hukumar zaben
  • Sanarwa daga gidan gwamnatin jihar Ribas ta nuna cewa Sufeta Janar na 'yan sanda ne ya ba jami'an umarnin sace kayayyakin zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ribas - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers da tawagarsa sun dura ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar (RSIEC) da ke birnin Fatakawal.

A safiyar ranar Juma'ar nan ne aka ce Fubara ya samu rahoton cewa wasu 'yan sanda sun fasa ofishin RSIEC domin sace kayan zaben ciyamomin jihar na gobe Asabar.

Kara karanta wannan

Fitattun 'yan siyasar Kudancin Najeriya da za su iya kalubalantar Tinubu a 2027

Fuba da tawagarsa sun dakile yunkurin 'yan sanda na 'sace' kayayyakin zaben ciyamomin Ribas
Gwamna da tawagarsa sun dakile harin sace kayayyakin zaben ciyamomin Ribas.
Asali: Twitter

Gwamna ya dakile shirin hana zabe

‘Yan sandan da ake zargin an turo su Ribas daga jihar Abia ne aka ce sun mamaye ofishin domin daukar kayan amma Fubara da mutanensa suka hana, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan jami'an gwamnati irin su shugaban ma'aikata, Edison Ehie, kakaki da 'yan majalisar Ribas masu biyayya ga gwamna Fubara sun je ofishin RSIEC domin dakile shirin.

Rahotonni sun nuna cewa jami’an ‘yan sanda karkashin jagorancin wani mataimakin kwamishinan rundunar na Ribas sun dura RSIEC da misalin karfe 1:00 na daren Juma’a.

Wata sanarwa da aka fitar da sanyin safiyar Juma’a ta hannun sakataren yada labaran gwamnan, Nelson Chukwudi, ta yi zargin cewa ‘yan sandan sun yi yunkurin sace kayan zaben.

'Yan sanda za su sace kayan zabe?

Sanarwar Nelson Chukwudi ta ce 'yan sandan sun yi yunkurin shiga babban dakin ajiye na hukumar RSIEC domin yin gaba da kayan zaben ciyamomi da za a gudanar gobe.

Kara karanta wannan

1 Oktoba: Rundunar yan sanda ta kara yawan jami'ai a Arewacin Najeriya

Ya yi zargin cewa Sufeto-Janar na ‘yan sandan ne ya bayar da umarnin a tura dakarun domin dauke kayayyakin zaben, inji rahoton Independent.

"Sai dai ba su cimma mugun nufinsu ba. Wasu 'yan bijilan sun sanar da manajan jami'an hukumar inda su kuma suka yi gaggawar sanar da gwamna halin da ake ciki.
"Nan da nan gwamnan ya jagoranci tawagar jami'an gwamnati, 'yan majalisa daga tarayya da na jiha, manyan masu ruwa da tsaki na siyasa suka dakile shirin."

- A cewar Nelson Chukwud.

Zabe: Zanga zanga ta barke a Ribas

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu matasan PDP sun jagoranci zanga zanga domin nuna fushi kan shirin zaben ciyamomi da kansilolin Ribas da ake shirin yi.

Masu zanga zangar sun dura ofishin hukumar DSS da 'yan sanda inda suka nemi jami'an da su nisanci zaben da Gwamna Siminilayi Fubara zai gudanar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.