ACF: Kungiyar Dattawa Ta Fadi Yadda Rashin Tsaro Ke Neman Shafe Arewa

ACF: Kungiyar Dattawa Ta Fadi Yadda Rashin Tsaro Ke Neman Shafe Arewa

  • Kungiyar ACF ta bayyana fargaba kan yadda rashin tsaro ke karuwa a dukkanin sassan Arewacin Najeriya
  • Shugaban kwamitin amintattun kungiyar, Alhaji Bashir Muhammad Dalhatu ya ce akwai babbar barazana a yankin
  • Ya yi takaicin yadda matakan yaki da rashin tsaro ba su dakile matsalar da ake fama da ita a Arewacin kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno - Kungiyar ACF ta bayyana damuwa kan karuwar rashin tsaro a sassan Arewacin kasar nan.

Shugaban kwamitin amintattun kungiyar, Alhaji Bashir Muhammad Dalhatu ne ya bayyana haka, inda ya ce lamarin akwai firgitarwa.

Dutse
ACF ta damu kan barazanar karuwar ta'addanci a Arewa Hoto: UGC
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Alhaji Bashir Muhammad Dalhatu na wannan batu ne a ziyarar jaje da ya kai Maiduguri, jihar Borno.

Kara karanta wannan

Kungiya ta fadawa Tinubu ribar da zai samu idan ya sasanta rikicin masarautar Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ACF ta damu da ta'addanci a Arewa

Jaridar Daily Post ta tattaro cewa kungiyar ACF ta ce rashin tsaro da ke addabar Arewa na zama babbar barazana ga rayuwa a yankin.

Shugaban kwamitin amintattun kungiyar, Alhaji Bashir Muhammad Dalhatu ya ce ana fama da yan tayar da kayar baya a Arewa maso Gabas.

Baya ga haka, akwai 'yan bindiga a Arewa maso Yamma da sauran bata-gari a Arewa ta Tsakiya da ke fama da rikicin makiyay da manoma.

ACF ta nemi kawowa Arewa karshen ta'addanci

ACF ta ce akwai babbar barazana matukar mahukunta su ka zuba ido a kan rashin tsaron da ya addabi yankin Arewacin kasar nan.

Kungiyar na ganin matakan tsaro da ake amfani da su ba su takawa yan ta'adda birki ba, saboda haka kungiyar ta nemi a sake dabarar yaki da ta'addanci a yankin.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya koka da karuwar talauci a Arewa duk da yan siyasarta na gwamnati

Sojoji na shirin dakile ta'addanci a Arewa

A wani labarin mun ruwaito cewa rundunar tsaron kasar nan ta ce dakarunta na namijin kokari wajen kawo karshen ayyukan ta'addanci a yankin Arewa da sauran sassan kasar.

Babban hafsan tsaron kasa, Janar Christopher Musa ne ya bayyana haka, ya kara da cewa abin da ya jinkirta nasara kan yan ta'addan shi ne tsoron kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.