Bayan Kashe Halilu Sububu, Hafsan Tsaro Ya Fadi Halin da Bello Turji Yake Ciki Yanzu
- Babban hafsan tsaron Najeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya jaddada cewa kwanakin fitinannen dan ta'adda Bello Turji a kirge suke
- Janar Christopher ya kuma ce a halin yanzu Bello Turji na cikin firgici sakamakon kashe ubangidansa watau Halilu Sububu da sojoji suka yi
- Babban hafsan tsaron ya ba da tabbaci cewa sojoji za su ci gaba da kai hare-hare kan 'yan ta'adda musamman a shiyyar Arewa maso Yamma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Babban hafsan tsaron Najeriya (CDS), Janar Christopher Musa, ya ce Bello Turji na cikin tashin hankali sakamakon hare-hare da sojoji ke kaiwa ‘yan ta’adda a Arewa maso Yamma.
Janar Christopher Musa ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai a gefen taron lacca na shekara-shekara da kamfanin NAN ya shirya a ranar Alhamis a Abuja.
"Bello Turji na cikin firgici" - Hafsun Tsaro
Babban hafsan tsaron ya bayyana cewa kisan Halilu Sububu da wasu kwamandojin ‘yan ta’adda da dama ya sanya fargaba a sansanin Turji inji rahoton NAN.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ka ga daga matakin da yake dauka, za ka gane cewa yana cikin fargaba. A baya za ka ga yana fitowa yana maganganu son ransa kamar shi kadai ne ke da iko.
“Yanzu ya san ba shi ne ke rike da ikon ba. Ya san lokaci ne kawai ke jiransa domin Halilu Buzu da aka kashe shi ne ubangidansa.
"Saboda haka yanzu da ya san kwamandan nasa ya tafi, ya san shi ne harin gaba, don haka shure shure ne kawai yake yi yanzu amma lokacinsa a kididdige yake."
- A cewar Janar Christopher.
Sojoji sun tsananta kai hare hare
Babban hafsan tsaron ya ce tuni dan ta'addan ya ketare iyakarsa. Ya ce sojoji za su ci gaba da kakkabe 'yan ta'adda a hare haren da suke ci gaba da kai wa.
Jaridar Vanguard ta rahoto shi yana cewa rashin tsaro na dadewa ne saboda talauci, jahilci da rashin shugabanci na gari a yankunan da matsalar ta yi kamari.
"Don haka suna da dimbin matasa da ba sa yin aikin komai. Za ga ka muna kashe wasu, wasu kuma na shiga tawagar 'yan ta'addan saboda ba su da ayyukan yi."
- A cewar babban hafsan tsaron.
Turji ya fadi sharadin zaman lafiya
A wani labarin, mun ruwaito cewa hatsabibin dan bindiga, Bello Turji ya fadawa gwamnati da jami'an tsaro sharadin dawo da zaman lafiya a jihar Zamfara.
A yayin da Bello Turji ya ce shi da yaransa ba sa tsoron mutuwa ya kuma shaidawa mutanen Zamfara cewa Gwamna Dauda Lawal da Bello Matawalle sun siyasantar da matsalar tsaro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng