Bayan Bidiyon Bello Turji, Tinubu Ya Tura Gargadi ga Yan Ta'adda, Ya ba Su Zabi 2
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura gargadi ga yan ta'adda yayin da rashin tsaro ya yi kamari a Arewacin Najeriya
- Mai girma Tinubu ya shawarci yan ta'addan da su ajiye makamansu ko su fuskanci fushin rundunar sojojin kasar
- Wannan na zuwa ne yayin da dan ta'adda, Bello Turji ya fitar da sabon bidiyo a ranar Litinin 30 ga watan Oktoban 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya tura sakon gargadi na musamman ga yan ta'adda kan ayyukansu musamman a Arewacin kasar.
Bola Tinubu ya gargadi yan ta'addan da su mika makamansu da watsar da ayyukan ta'addanci ko su fuskanci hukunci.
Bola Tinubu ya gargadi yan ta'adda a Najeriya
Shugaban ya bayyana haka ne yayin wani babban taro da aka gudanar a birnin Abuja a yau Alhamis 3 ga watan Oktoban 2024, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman a bangaren tsaro, Mallam Nuhu Ribadu.
Shugaban kasar ya sha alwashin kawo karshen yan ta'addan duba da yadda sojoji suka shirya dakile su.
Yan sanda sun sha alwashi kan ta'addanci
A bangarensa, babban sifetan yan sanda, Kayode Egbetokun ya bayyana himmatuwarsa wurin yaki da ta'addanci.
Egbetokun ya ce rundunar ba za ta taɓa gajiyawa ba wurin tabbatar da dakile matsalolin rashin tsaro da ke damun kasar.
"Rundunar yan sanda na daga cikin tsarin, ba za mu gajiya ba wurin tabbatar da kawo karshen rashin tsaro da ke damun al'umma."
- Kayode Egbetokun
Sububu: Bello Turji ya sako sakin bidiyo
Kun ji cewa kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji ya fitar da sabon bidiyo a ranar Litinin 30 ga watan Satumbar 2024.
Dan ta'addan ya yi magana kan kisan Halilu Sabubu da sojoji suka yi inda ya bayyana shi a matsayin mai gidansu.
Turji ya yi ta'aziyyar kisan Sabubu inda ya ce hakan kwata-kwata ba zai kashe musu guiwa ba idan ba a bar kashe musu yan uwa ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng