Sanusi II Vs Aminu: Hayaniya Ta Ɓarke da Nuhu Ribadu Ya Kira Sunan Sarkin Kano a Wani Taro
- Mutane sun ɓarke da tafi a lokacin da mai ba da shawara kan tsaron ƙasa, Nuhu Ribaɗu ya kira Aminu Ado Bayero da sarkin Kano
- Rahotanni sun nuna lamarin ya faru ne a wurin wata lacca da aka shirya a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis da basaraken ya halarta
- Har yanzu dai rikicin sarautar Kano bai ƙare ba domin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado na ci gaba da nuna iko da gidan dabo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribaɗu ya tayar da ƙura yayin da ya kira Aminu Ado Bayero a matsayin sarkin Kano a wurin taro.
Idan ba ku manta ba a watan Maris na 2020, tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya tsige Muhammadu Sanusi II tare da nada Aminu Bayero a matsayin sarki.
Sai dai bayan shekaru hudu da faruwar hakan, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kori Aminu tare da maido da Muhammadu Sanusi II kan karaga, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka saka Ribadu a rikicin sarautar Kano
Gwamna Abba ya sauke Aminu a lokacin da ba ya cikin jihar to amma daga bisani ya koma Kano inda ya tare a ƙaramar fadar Nassarawa, ya ci gaba da zaman sarauta.
A lokacin mataimakin gwamnan Kano, Aminu Gwarzo, ya yi zargin cewa Nuhu Ribadu ne ya kitsa dawowar Aminu ta hanyar ba shi jiragen sama biyu su rako shi.
Bayan ya yi barazanar kai karar Aminu Gwarzo kan wannan zargi, mataimakin gwamnan ya fito ya janye kalamansa.
Nuhu Ribaɗu ya kira Aminu da sarki a Abuja
Da yake jawabi a wurin wata lakca kan tsaro da hukumar dillancin labarai NAN ta shirya karo na farko a Abuja ranar Alhamis, Nuhu Ribaɗu ya kira Aminu Ado a matsayin sarkin Kano.
Yayin da yake ambatar manyan bakin da suka hallara a wajen taron, Ribadu ya ce, “Muna tare da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.”
Wannan kalamai na sa na kiran Aminu a matsayin sarkin Kano ya jawo mutanen da ke cikin ɗakin taron suka ɓarke da hargowa tare da tafi.
Kalaman Ribadu su fara jawo ce-ce-ku-ce
Wani mai goyon bayan basaraken, Rabiu Uba Danzainab ya wallafa bidiyon mai tsawon dakika 33 a shafinsa na X (@rabiuuba4).
Rabiu Uba ya haɗa da cewa, "Ribaɗu ya ambaci sarkinmu a matsayin halastaccen Sarkin Kano."
Amma wani mai amfani da manhajar X, Ahmed Idris ya maida masa martani da cewa, “Sarkin APC ba."
Har ila yau, wani mai suna @StudentYahaya, ya ce, "Kotun da ke da cikakken iko ce kaɗai za ta yanke hakan ba Ribaɗu ba."
Kotu ta shirya hukunci kan gyara fadar Nassarawa
A wani labarin kuma babbar kotun Kano ta zabi ranar 10 ga watan Oktoba, 2024 domin yanke hukunci a ƙarar da aka nemi dakatar da gyara fadar Nassarawa
Gwamnatin Kano ta buƙaci kotun ta hana Sarki na 15, Aminu Ado Bayero aiwatar da shirinsa na gyaran fadar da yake ciki yanzu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng