Mutuwar Fitacciyar Ƴar Jarida Ya Girgiza Gwamnan Kano, Ya Aika Sako ga Iyalan Kilishi

Mutuwar Fitacciyar Ƴar Jarida Ya Girgiza Gwamnan Kano, Ya Aika Sako ga Iyalan Kilishi

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nuna kaduwarsa bayan samun labarin rasuwar fitacciyar 'yar jarida, Hajiya Fatima Kilishi Yari
  • An rahoto cewa Hajiya Fatima Kilishi ta rasu ne a ranar Alhamis, 3 ga watan Oktoba ta na da shekaru 79 a duniya bayan gajeruwar jinya
  • Daga cikin 'ya'yan da Hajiya Fatima ta bari, akwai mai tallafawa Gwamna Abba ta fuskar hulda da jama'a na kasa da kasa, Hon. Muhammad Jamu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Allah ya karbi rayuwar Hajiya Fatima Kilishi Yari wadda aka fi sani da Fatima Yusuf a lokacin da ta ke aiki da gidan watsa labarai na BBC Hausa.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya koka da karuwar talauci a Arewa duk da yan siyasarta na gwamnati

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nuna kaduwarsa game da rasuwar fitacciyar 'yar jaridar awanni bayan da sanar da rasuwarta a ranar Alhamis.

Gwamnan jihar Kano ta yi ta'aziyyar rasuwar Hajiya Fatima Kilishi
Gwamnan Kano, Abba Yusuf ya mika sakon ta'aziyyar rasuwar Hajiya Fatima Kilishi. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Abba ya kadu da rasuwar Kilishi

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, gwamnan Kano ya yi alhinin rasuwar tsohuwar ‘yar jaridar wadda ya ce ta rasu a ta na da shekaru 79 a duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hajiya Fatima Kilishi wadda ta rasu bayan fama da rashin lafiya ta fara aiki da sashen Hausa na BBC a birnin Landan a shekarar 1976 kuma ta yi aiki a gidan rediyon Kano a 1980.

Gwamna Abba ya ce:

"Marigayi Hajiya Fatima Yari ta rasu ta bar ‘ya’ya da jikoki, daga 'ya'yanta akwai akwai mai ba ni shawara na musamman kan hulda da jama’a na kasa da kasa, Hon. Muhammad Jamu Yusuf."

Kara karanta wannan

Murnar samun 'yanci: Gambo Sawaba da fitattun mata 2 da su ka jijiga siyasar Najeriya

Gwamna ya yiwa Kilishi addu'a

Hajiya Fatima Kilishi Yari ta kasance mai fafutukar ganin ci gaban mata kuma 'yar jarida da ta ba da gudunmawa sosai wajen wayar da kan mata a lokacin aikinta.

"Amadadin gwamnati da al'ummar jihar Kano, ina addu'ar Allah ya jikanta da kuma sanya ta a cikin Al-Jannatul Firdausi."

- A cewar Abba Yusuf.

Gwamna Abba ya kuma roki Allah ya tausasa zukatan iyalan Hajiya Fatima Kilishi bisa wannan babban rashi da suka yi.

Abba ya yi ta'aziyyar 'yan sanda

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kano Abba Yusuf ya mika sakon ta'aziyya ga rundunar 'yan sanda bisa rasuwar wasu jami'an rundunar a hatsarin mota.

An rahoto cewa Abba Yusuf ya kuma ba iyalan kowane dan sandan da ya rasu a hatsarin kyautar N500,000 domin nuna damuwar gwamnatin jihar Kano kan halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.