Ta'addanci: Rundunar Tsaro Ta Yi wa Sanata Martani kan Neman Agajin Sojojin Haya

Ta'addanci: Rundunar Tsaro Ta Yi wa Sanata Martani kan Neman Agajin Sojojin Haya

  • Rundunar tsaro ta kasa ta ce dauko sojojin haya ba zai kawo karshen yan ta'adda a kasar nan ba
  • Babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa ne ya bayyana bayan Sanata Ali Ndume ya bayar da shawarar dauko sojojin
  • Janar Christopher Musa ya ce zuwa yanzu, dakarun sojan Najeriya sun hallaka yan ta'adda akalla 300

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Babban hafsan tsaron kasar nan, Janar Christopher Musa ya bayyana yadda za a kawo karshen ta'addanci a Najeriya. Janar Christopher Musa ya ce dauko sojojin haya domin fatattakar yan ta'adda ba zai magance matsalar kamar yadda wasu ke tunani ba.

Kara karanta wannan

Bello Turji ya tsorata, ya nemi kawo karshen ta'addanci a yankin Arewa

Janar
Rundunar tsaro ta ce ba a bukatar sojojin haya a Najeriya Hoto: Nigerian Army HQ
Asali: Facebook

Arise TV ta wallafa babban hafsan tsaron na cewa jami'an rundunar sojan kasar nan na samun nasara kan yaki da yan ta'adda, kuma sannu a hankali za a magance matsalar tsaro.

Janar Christopher Musa ya bayyana cewa ko a kasashen Mali da Afghanistan da aka dauki sojojin haya, ba a shawo kan matsalar da ake fatan magancewa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin rashin amfanin sojojin haya a Najeriya

Babban hafsan tsaron kasar nan, Janar Christopher Musa ya ce ana yaki da yan ta'adda masu basaja a cikin jama'a, wanda ba zai yiwu a yake su gaba da gaba ba.

Ya ce duk dan ta'addan da ba ya rike da bindiga ko makami, ba lallai ne ta kallo daya a fahimci dan bindiga ne ba, saboda haka yaki da irinsu ke da wahalar gaske.

Rundunar tsaro ta ce sojoji na kokari

Kara karanta wannan

Karshen alewa: Yan ta'adda sun ji wuta, sun shiga hannun yan sanda a Abuja

Janar Christopher Musa ya bayyana cewa zaratan sojojin kasar nan sun hallaka iyayen gidan yan ta'adda akalla 300 a fadin kasar nan. Ya kara da cewa yanzu haka ana horas da jami'an tsaron kasar nan a Amurka da Turai domin kara samun kwarewar kawar da yan ta'addan da ke Najeriya.

Ta'addanci: An shawarci gwamnati kan sojojin haya

A baya kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya ba gwamnatin Bola Ahmed Tinubu shawarar dauko sojojin haya domin karar da yan ta'addan da suka hana jama'a sakat.

Sanata Ali Ndume na ganin sojojin hayan daga kasashen ketare na da manyan makaman da ake bukata wajen lallasa hatsabiban yan ta'addan da su ka addabi Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.