Bello Turji Ya Tsorata, Ya Nemi Kawo Karshen Ta'addanci a Yankin Arewa
- Fitinannen dan ta'adda Bello Turji ya magantu kan kokarin rundunar sojan kasar nan na kawo karshensa nan kusa
- Dan ta'addan da ya addabi mazauna Zamfara da kewaye ya ce mutuwa ba ta tsorata shi, duk da kashe abokan dabarsa
- Ana zargin ya tsorata, domin dan ta'addan ya nemi a zauna da gwamnati domin kawo karshe ayyukan ta'addanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara - Rikakken dan ta'adda, Bello Turji ya kalubalanci rundunar tsaron kasar nan, inda ya ce mutuwa ba ta ba shi tsoro.
Ya bayyana haka ne daga maboyarsa yayin da jami'an tsaron kasar nan ke luguden wuta kan yan ta'adda har aka yi nasarar kashe abokansa.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Bello Turji na cikin miyagun yan ta'adda 43 da gwamnatin kasar nan ke nema ruwa a jallo a yankin Arewa maso Yammacin kasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bello Turji ya nemi zama da gwamnati
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa Bello Turji, fitinannen dan ta'adda da jami'an kasar nan ke kokarin shafewa daga doron kasa ya nemi zama da gwamnatin tarayya.
A wani bidiyo da ya wallafa a baya-bayan nan, ya yi kira ga gwamnatin Tinubu kan a zauna domin kawo karshen ta'addanci a jihar Zamfara.
Dan ta'adda Bello Turji ya shirya mutuwa
A wani bidiyo da Bello Turji ya fitar, ya ce kisan mai gidansa, Halilu Sububu ba zai sa ya ja bakinsa ya yi shiru ba.
Ya ce wadanda ke cewa an kusa kashe shi ba za su dauwama a duniya ba, domin shi ma a shirye ya ke da a kashe shi ko yaushe daga yanzu.
Gwamna ya fadi lokacin kashe Bello Turji
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa ana dab da kawo karshen yan fitinannen dan ta'adda Bello Turji da ire-irensa da su ka hana jihar zaman lafiya.
Gwamna Dauda Lawan Dare ne ya bayyana haka, inda ya danganta karuwar rashin tsaron da ake fuskanta a Zamfara da ayyukan hakar ma'adanai da ake yi a wasu kauyukan jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng