Gyaran Haraji: Tinubu Zai Rusa Hukumar FIRS, Ya Aika Kudurori 4 ga Majalisar Wakilai
- A ranar Alhamis, kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen ya karanta wata wasika da shugaban kasa Bola Tinubu ya aiko masu
- A cikin wasikar, Tinubu ya gabatarwa majalisar kudurori hudu da suka shafi sake fasalin haraji inda ya bukaci amincewarsu da gaggawa
- A cewar shugaban kasar, kudurorin da ya gabatar an tsara su ne bisa tsari da kuma manufofin gwamnatinsa na gyara tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatarwa majalisar wakilai wasu kudirori hudu na sake fasalin haraji domin tantancewa da kuma amincewa da su cikin gaggawa.
Bola Tinubu ya gabatar da kudurorin ne a cikin wata wasika da kakakin majalisar wakilai Abbas Tajudeen ya karanta a zauren majalisar a ranar Alhamis.
Shugaban kasar ya bayyana cewa an tsara daftarin kudirorin ne bisa tsari da manufofin gwamnatinsa, a cewar rahoton Arise News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga bayanain kudurorin a kasa:
1. Kudurin dokar harajin Najeriya
An samar da kudurin dokar harajin Najeriya na shekarar 2024 domin ya samar da aikin kasafin kudin haraji a kasar nan.
2. Kudurin dokar kula da haraji
Kudirin kula da harajin zai samar da tsayayyen tsari na shari'a ga duk harajin kasar tare da rage rigingimun da ake samu daga tattara harajin.
3. Kudirin kafa hukumar harajin Najeriya (NRS)
Wannan kudurin dokar zai soke dokar da ta kafa hukumar tara kudaden shiga ta kasa (FIRS) tare da kuma kafa hukumar tara haraji ta Najeriya (NRS).
4. Kafa hukumar haraji ta hadin guiwa
Kudurin dokar kafa hukumar hadin guiwa kan kudaden haraji zai samar da kotun haraji da mai kula da korafe korafen haraji.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce kudirorin za su karfafa hukumomin hada-hadar kudi a kasar tare da daidaita ayyukan tattara haraji da manufar gwamnati.
Tinubu ya shilla kasar Birtaniya
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shilla birnin Landan na kasar Birtaniya inda zai shafe tsawon kwanaki 14.
A ranar Laraba ne fadar shugaban kasar ta fitar da sanarwar cewa Tinubu zai shafe makonni biyu a Landan ya na hutawa tare da bitar manufofin gwamnati.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng