An Kara Gano Gawarwakin 'Yan Maulidi da Jirginsu Ya Kife a Neja

An Kara Gano Gawarwakin 'Yan Maulidi da Jirginsu Ya Kife a Neja

  • An kara gano gawarwaki takwas na yan maulidi da kwale-kwalensu ya kife a jihar Neja da taimakon yan ninkaya
  • Yawan wadanda aka gano gawarwakinsu cikin mutum 150 da ake fargabar sun rasu yanzu ya kai 24 a kauyen Nejan
  • Darakta Janar na hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, i Abdullahi Baba Arah ya ce ana cigaba da aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Niger - Masu ninkaya a jihar Neja sun gano karin mutane takwas daga cikin masu zuwa maulidi da kwalekwalensu ya kife a makon nan.

Mutane akalla 300 ne su ka hau wani kwale-kwale daga yankin Mundi, inda jirgin ya kife a Gbajibo da ke karamar hukumar Mokwa a jihar Neja.

Kara karanta wannan

'Ku zauna a shirye,' NLC ta yi zazzafan gargadi a dukkan jihohi kan karin albashi

Niger
An gano karin gawarwakin yan maulidi 8 Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa a yau Alhamis aka ci gaba da aikin zakulo wasu daga cikin gawarawakin mutane 150 da su ka bata bayan kifewar kwalekwalen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gawarwakin 'yan maulidi a Neja ya karu

Jaridar Solacebase ta wallafa cewa an samu karuwar gawarwakin masu zuwa taron maulidi a jihar Neja zuwa 24, bayan an gano wasu takwas a yau.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Neja ce ta tabbatar da karin gawarwakin a yau, yayin da ake ci gaba da kokarin tsamo wasu daga wadanda su ka rasu domin suturta su.

An binne wasu gawarwakin yan maulidi

Darakta Janar na hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, Alhaji Abdullahi Baba Arah ya ce tuni aka yi jana'izar mutane 16 da aka gano bayan hadarin jirgin.

Daga cikin wadanda aka gano, akwai mata biyu da maza 14, kuma an binne su a yankin Gbajibo ranar Laraba.

Kara karanta wannan

NSEMA: An bayyana halin da ake ciki bayan jirgin ƴan Maulidi ya yi hatsari

Yan maulidi 150 sun bace a Neja

A baya mun ruwaito cewa an shiga fargaba a Neja da kwalekwalen da ke dauke da mutane kimanin 300 ya kife a hanyarsu ta zuwa bikin maulidi a Gbajibo.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar (NSEMA), Abdullahi Baba-Arah ya bayyana cewa ana cikin zullumin akalla mutane 150 sun rasa rayukansu a hadarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.