Nnamdi Kanu Ya ba Gwamnatin Tarayya Zabi kan Tuhumar Ta'addanci da Ake Yi Masa

Nnamdi Kanu Ya ba Gwamnatin Tarayya Zabi kan Tuhumar Ta'addanci da Ake Yi Masa

  • Shugaban haramtacciyar kungiyar yan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu ya mika bukatu ga gwamnatin tarayya
  • Jagoran lauyoyin Kanu, Alloy Ejimakor ya nemi gwamnati ta janye tuhumar da ake yi wanda su ke wakilta a kotu
  • Lauyoyin sun ba gwamnati zabin bayar da belin Nnamdi Kanu idan har ba za a iya janye tuhumar da ake yi masa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Lauyoyin shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu sun mika bukatarsu ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Lauyoyin, karkashin jagorancin Aloy Ejimakor sun baukaci gwamnatin tarayya ta janye tuhumar ta'addanci da ake yi wa Nnamdi Kanu.

Kara karanta wannan

Murnar samun 'yanci: Gambo Sawaba da fitattun mata 2 da su ka jijiga siyasar Najeriya

Tinubu
Nnamdi Kanu ya nemi gwamnati ta janye tuhumar da ta ke masa Hoto: Kola Suloiman/Bola Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa lauyoyin sun ba gwamnati zabi da ta bayar da belin Mazi Kanu idan har ba za ta janye tuhumar ta'addancin ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nnamdi Kanu ya fadawa gwamnati ta janye tuhumarsa

Lauyoyin Nnamdi Kanu sun bayyana cewa sun bukaci gwamnati ta janye tuhumar ta'addanci ko bayar da belin wanda su ke wakilta saboda wasu dalilai.

Barista Aloy Ejimakor ya ce bayar da belin Nnamdi Kanu zai ba shi damar shirin tunkarar tuhumar da gwamnatin kasar nan ke masa na cin amanar kasa.

Lauyoyi sun ce Nnamdi Kanu na cikin wahala

Daya daga cikin lauyoyin Nnamdi Kanu, Barista Nnaemeke Ejiofor ya bayyana wanda su ke wakilta na cikin mawuyacin hali a hannun jami'an DSS.

Lauyoyin sun yi bayanin cewa matakin da su ka dauka na neman Alkali ta janye kanta daga shari'ar ya biyo bayan fargabar za a yi masu rashin adalci.

Kara karanta wannan

Kungiyoyi a Kaduna sun barranta da zanga zangar 1 ga watan Oktoba

Nnamdi Kanu ya nemi sulhu da gwamnati

A baya kun ji cewa jagoran haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya bayyana cewa a shirye ya ke ya tattauna da gwamnatin tarayya kan zargin ta'addanci da ake yi masa.

Jagoran tawagar lauyoyin Mista Kanu, Alloy Ejimakor ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa sashe na 17 na dokar babbar kotun tarayya ya bayar da damar cimma masalaha ta tattaunawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.